✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kira ga wakilan majalisun jihohin Arewa

Harkar saye, sayarwa bada haya ko aron gidaje da shaguna d filaye ta zama sakaka, ta yadda a yanzu ake yin ta a tsakanin mai…

Harkar saye, sayarwa bada haya ko aron gidaje da shaguna d filaye ta zama sakaka, ta yadda a yanzu ake yin ta a tsakanin mai shi da mai so ko kuma tsakanin dillalai da mai karba ba tare da sanin mai unguwa ko fagaci ko limamin gari ba, kamar yadda abin yake a da. Hakan na daya daga cikin manyan abubuwan da suke kara kawo kalubale a fannin tsaro musamman matsalar garkuwa da mutane da satar yara da sauran ayyukan barna da suke yaduwa a tsakanin al’umma.

Kasancewar an saki waccan hanya ce ake samun miyagun mutane suna shigar burtu suna shiga cikin unguwanni da kauyuka da birane suna sayen filaye su gina ko su sayi ginannun gidaje su zauna ko kuwa su yi hayar gida ko shago su shiga ciki su yi ta amfani da su suna fakewa da guzuma suna harbin karsana.

Yana da kyau wakilan majalisun dokokin jihohin Arewa su yi wata doka da za ta tilasta wa mai saye ko mai sayarwa ko dillali cewa dole sai sun gabatar da kawunansu a gaban sarakunan gargajiya yankin da suke don gabatar da wanda zai saya ko hayar wani gida ko shago ko fili ko gona in bako ne a wannan wuri kuma yana son saye ko hayar wata kadara. Ta yadda su sarakunan za su rubuta su ajiye muhimman bayanai game da wanda zai saya ko mai daukar hayar. Wadannan bayanai za su iya kunsar; shin wane ne shi mai saye ko hayar”? Me zai yi da abin da yake son saye ko hayar? Daga ina ya fito kuma mece ce sana’arsa?

Haka kuma su rubuta su ajiye sunan garinsa na asali, sunayen danginsa da iyalinsa kai har da tarihin rashin lafiya ko nakasa da shi ko iyalinsa suke da shi. Sannan su samu akalla hotunansa da na iyalinsa.

Wannan doka idan aka aiwatar da ita za ta taimaka wajen takaita wasu laifuffuka da ayyukan ta’addanci da bakin fuska kan yi ta hanyar samun mafaka cikin al’ummar da ba su da masaniya game da boyayyiyar manufarsu, wanda hakan yana cutar da jama’a ta hanyoyi daban-daban.

Iro Surajo, Abuja

(0816 343 9197)