Manuniyar munin yanayi
A kasashen duniya aka yi
Haurobiya kan babban layi
An dai samu tsautsayi
Mahukunta me kuke tsimayi
Al’umma na jin jiki
Wadansu na ta biki
Adon-gari an rambada jam baki
’Yan lalle ana ta sakin baki
Tsofaffi na cike da mamaki
Kimanta kuncin kaskantar kasa
Kundumbalar ’yan wasa
Karajin masu sa-in-sa
Karfin kwanjin kwankwasa kwarkwasa
Karfa-karfar kasurar kusa
Kudin cizo kwarkwata da kuma
Kamuya-muyar karma-karma
Kyankamin kyama
Kunzugun kazama
Kauyuka da birane ana hamma
Haurobiyawan fama
Hakilon dama-dama
Hankoron hadama
Hayagagar masu takama
Harbin karsana da guzuma
Macizai da kunami
Cizo da harbin karin kaimi
Miyagu masu fashi da mukami
Gyambo ne ake ta fami
Farmakin magabta da makami
An fitar da jaddawali
Alkaluma ne a fili
Yawan marasa muhalli
Adadin marasa hankali
Da dukiya ake fatali
Wayyo Direban alli
Dalibai an shirya musu kwali
Makaranta na kyalkyali
Koyi-ka-koyar ba fasali
Shagabanni na fi’ili
Yamadidi yai yawa
Yarfen yekuwa
Yankar yakuwa
Yanayin yadon yadiyar yadawa
Yafucen ’yan yawa
Giringidimin gigiwar giwaye
Gogoriyon gauraye-gauraye
Gayun gundumar gwanaye
Gumurzun gwauraye
Garnakakin gaye-gaye
Tukin tuwo
Damun dawo
Naman dabbar kiwo
Tiyar hatsin awo
Akushi kowa ya kawo
Masana fannonin ilimi
Ai watsattswake da wasali
Ku sa ai aiki da hankali
Dukiya ta zam tattali
Zalunci ya daina tsunkuli
A haska fitila
Kowa ya sakata ya wala
Al’umma ta ji ba wahala
A samu karsashin kawar da kasala
Zukata su faranta ba hassala
Mu daina ci wa juna kwala
Kowa ya fice daga matsala
A tarwatsa masu laluben galala
Don su dinka galleliyar galila
Wai sun samu salala
A daina yi musu talala
Su daina samun walwala
A tsula musu bulala
Sui ta lalala
Sai arzikin kasa ya malala
Kasarmu ta kayatar
Ba wanda zai kaskantar
Kyawunta yai nono tar-tar
Mun bar sha wa juna mur
Miyagun ta’adu mun ce tir
A kawar da juhala
Ai fafutikar tabbatar da adala
Faskekiyar fahimta ce falla-falla
Da karatu dalla-dalla
Sai kowa ya kula
Kowa ya bi umarni
A kiyaye hani
Mui wa juna tuni
Kar ai sabani
A daina laifi babba da kankani
Kyakkyawar ta’ada
Bin ka’ida
A riski gwaggwabar fa’ida
Rubutun alkalami da tawada
In an gaza karatu malumma su tada
A bi doka
Ka da kowa ya koka
A kauce wa kiki-kaka
Balaguro a tattaka
Ba shakkar mugu mai fatattaka
Karshen karkarewar marisar Maris da farkon tunkarar Wata-a-farin-lilon shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa, ana ta yamadidi da yarfen yadon yadiyar yadawar ’yan yawa kan yadda MANUNIYAR MUNIN MATSAYI ta dora Haurobiya a babban layi. Ta yiwu a ce lamarin dai ba wani tsautsayi ba ne, don haka sai mu ce da mahukunta me kuke tsimayi?
Jerin kasashen a cewar Jam’in jami’an Jami’ar John Hopkins, su ne Benen-zuwan-lalala wadda ta rike kambinta a tsawon shekarun 2015 da 2016 da 2017 da 2018 da farfajiyar Iraniyawa da Barazana-da-zilliya da Turakun turka-tukar tunkude kiyayya ko in ce Turakun tarairayar uwa da ’ya’ya .
Ma’aunin munin matsayin muhallin mutane na bisa kan doron zaman dirshan da kashe fatari a tsakankanin al’ummar kasa da tsulin tsawwalar tsadar rayuwa, da ARON ASIN ASUSU, tare da dauke kimar dukiyar da ake hada-hadar kasuwanci ko kaso-kaso wawanci da ita a kasa. Wannan dai duk irin tsirfarsu Jam’in Damo: Je-fi Mugun, wanda ya taba fitar da Haurobiya daga jerin jadawalin manuniyar kimar bunkasar tattalin arzikin kasa ba da dadewa da darewar Baban-burin-huriyya bisa karagar mulki. Sannan an samu kwata irin wannan tsurkun tsirface-tsirface daga uwargida mai Langar Ligidin lallaga lamunin lumana ligi-ligi.
’Yan makaranta sai mu kara bitar LANGAR LIGIDIJN LAGAD da JAMI’IN DAMO: JE-FI MUGUN, tare da miyagun ayyukan kassara kasa da aka tsuwirwirta a Hauyrobiya, musamman HALIN-BURTU: A BADDA KAMA A YI BARNA da BASUSSUKAN WUNI-WUNI irin na ’YAN UWAN DA BA SU DA WANI da dai makamantansu.
Haurobiyawa, cikin shekara ta dubu karamin lauje da kofar hanci Bakin Birtaniyawan Cece-ku-ce da jaridar Gadin-yana ta Haurobiya da sauran kafafen yada kwakwazo da watsattsaken labaran duniya, sun taba baje manuniyar alkaluman jadawalin da ya tabbatar da gwaggwabar alamar FARA’AR FUSKOKIN FURANNI a Haurobiya. Wata manuniyar ta nuna kasar nan a mataki na babban lauje a fadin Ifrikiyya, yayin da aka ce a daukacin fadin duniya ita ce ta manuniyar kasa da sili. Koda yake dai a zamanin mulkin mulaka’u ne na jam’iyya mai danboto da sanda jirge.
’Yan jam’iyya mai danboto da sanda jirge sun ayyana cewa rahoton Jami’in jami’an jam’in jama’ar Jami’ar John Hopkins na nuni da cewa Haurobiya na kara kaskanta kasa-kasa a harkar tattali. Don haka ni ma na ce su kuwa a zamanin mulkin mulaka’unsu Haurobiya ta yi matukar kasura a FANTAMAWAR FACAKAR FATALIN FATATTAKA FAMA-FAMAI da DAFDALAR DAULAR DANNE DALOLI. Kuma DANNIYA DA MURDIYYAR da ta fi fice ita ce ta MACE-DA-ZANE DA SAMUN-BOM-DA-SAUKI.
A wajen bikin yaye daliban jam’in jama’ar jami’ar Jihar Lallaga-sisi a baban birnin su Lasisi, mataimakin Baban-burin-huriyya, Usainin-Babajo ya nuna wa al’umma yadda ake tarairayar masu koyon watsattsake da fallen shafukan wagagen littattafai, inda ake dundume musu kururu da nagge da karsana dubu dari baban lauje da tsuntsayen miya dubu sili da kofar hanci da madambaci da ’ya’yan kaji wadanda ba a kyankyashe ba, har malala manuniya sama da dubu dari madambaci.
Hakika wannan martani ne ga Jami’in Jami’an jam’in jama’ar Jami’ar John Hopkins da hamshakan ’yan jam’iyya mai danboto da sanda jirge da ke murmushin murnar rahoton manuniyar mummunan matsayi ga kasar Haurobiya.
Ita dai wannan rayuwa kusan kowa ya san akwai bagiren da wani ke kwararar da kwallar hawaye, yayin da wadansu ke furkaniyar farin cikin ruguntsimin biki.
Hakika alkaluman jimamin jadawalin jinjina jajjagen jaga-jagar jigata jelen jalli-jogar jama’a a Haurobiya ta yiwu shaci-fadi ne ko zuki-ta-malle kama-kolo ka hada shi da zomo. Domin idan ba haka ba me ya sanya sai lokacin da su Baba-ojo da Gudun-loko suka jigata al’umma aka ce manuniyar farin farin-cikin fara’ar fuskokin furanninmu ta kasura?