Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin kifaye . Labarin ya kunshi illar rashin bin shawara. A sha karatu lafiya.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi
A wani jeji akwai wani kada mai kirki da ke rayuwa a kusa da wani rafi. A kullum sai ya baiwa kifayen shawarar su daina yawan fitowa bakin rafi domin wata rana za a iya kama su.
Kifayen sun raina kadan inda suke guna-guni suna fadin cewa: “mun gaji da shawarar da wannan kada ke bamu ai gara ya kyale mu don mu sakata mu wala ”. Sai suka shiga yin wani irin iyo na yanga don baiwa kadan haushi.
Rannan wasu sun zo wucewa sai suka ga kifaye da yawa a rafi. Sai dayan ya tambaya “da ma akwai kifaye masu yawa a wannan rafin shi ne ba mu sani ba?” sai dayan ya ce “yakamata mu zo gobe mu kwashe kifayen nan”.
Ashe kadan na saurarensu. Suna tafiya sai kadan ya shiga cikin kogin don bai wa kifaye labarin da ya ji. Sai suka kwashe da dariya suka ce “lallai, ta yaya za su iya kama mu? Ai mutane da dama sun sha zuwa don kama mu amma ba su samu nasara ba don haka, wadannan biyun ma ba su isa su kama mu ba.
Washe gari wadannan mutane suka zo da katon kwanduna suka kwashe kifaye kaf. Nan take daya daga cikinsu ya ce “ da mun bi shawarar kada da hakan bai faru da mu ba.