✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kidayar ’yan Najeriya za ta lakume N190bn a badi — Majalisa

Buhari kadai muke jira ya sa ranar da za a fara aikin.

Majalisar Dattawa ta bayyana cewa fiye da Naira biliyan 190 aka kasafta cewa za a kashe wajen gudanar da aikin kidayar ’yan Najeriya a badi.

Kwamitin Majalisar mai kula da sha’anin Hukumar Zabe da Hukumar da ke bayar da shaidar dan kasa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Kwamitin, Sanata Sahabi Alhaji Ya’u ya ce wannan na zuwa ne bayan Hukumomin da ke karkashin kulawar kwamitin suka kammala kare ba’asin kasafin kudaden da za su batar a badi.

A cewarsa, “fiye da naira biliyan 190 aka kiyasta za a batar domin gudanar da aikin kidayar ’yan Najeriya, wanda a yanzu umarnin Shugaban Kasa kawai ake tsimayi ya furta lokacin da za a fara gudanar da wannan aiki.

Dangane da batun la’akari da cewa 2022 shekara ce da bayanta za a gudanar da Babban Zaben Kasa, Sanata Ya’u ya ce, wannan shi ne lokaci mafi dace na gudanar da aiki.

“Sun riga sun kammala duk wasu lissafe-lissafe a kan hakan kuma Shugaban Kasar a shirye yake a gudanar da aikin kidayar ’yan kasa a 2022.”

Ana iya tuna cewa, tun kidayar ’yan kasa da aka gudanar a shekarar 2006 ba a sake gudanar da wata ba.

Yawan al’umma na daga cikin manyan abubuwan da ake la’akari da su a Najeriya, wajen rabon arzikin kasa tsakanin jihohin kasar 36.