An zabi kocin Najeriya Stephen Keshi a matsayin na 14 a jerin masu horarwa a sassan duniya kamar yadda wata mujalla da Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) bangaren masu horar da kwallo ta sanar.
Jadawalin ya nuna Keshi ne ya fi kowane koci nuna kwazo daga Nahiyar Afirka bayan ya shiga gaban korarren kocin Ghana Kwesi Appiah.
A jadawalin, kococi 50 da ke sahun gaba an zabo su ne daga kasashen da suka halarci gasar cin kofin duniya a Brazil, inda aka zabi 15 din farko daga kasashen da suka fi nuna kwazo a gasar.
Kocin Jamus Joachin Low ne na farko bayan kasarsa ta samu nasarar lashe gasar cin kofin duniya a Brazil yayin da kocin Sifen bincent Del Boskue ya kasance a matsayi na biyu sai kocin Uruguay Oscar Tabarez a matsayi na uku.
Mujallar takan kada kuri’a don zabar kococin da suka fi nuna kwazo ne daga lokaci zuwa lokaci don sanar da duniya matsayin kowane daga cikinsu.
Keshi ne na 14 a duniya 1
An zabi kocin Najeriya Stephen Keshi a matsayin na 14 a jerin masu horarwa a sassan duniya kamar yadda wata mujalla da Hukumar shirya kwallon…