Gwamnatin kasar Kenya ta ba da kai boyi ya hau wajen sake mayar da tallafin man da ta janye bayan jama’ar kasar sun tayar da kayar baya kan tsadar rayuwa a kasar.
Gwamnatin dai ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin ne har na tsawon kwanaki 30 masu zuwa.
- Kotun Amurka ta samu Trump da laifin tayar da rikicin zabe
- Faccala ta lakada wa faccalarta duka da itace a Kano
Tun lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasar a watan satumbar bara, William Ruto ya janye tallafin da ake biya a man fetur da masara da fulawa, wadanda ya gada daga wanda ya karbi mulki a hannunsa.
Shugaban dai a wancan lokacin ya ce ya gwammace ya bayar da tallafi a bangaren masana’antu ba wai a fannin abubuwan da ake amfani da su na kai tsaye ba.
Ya kuma ce an dauki matakin ne da nufin rage yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa a daidai lokacin da kasar ke fafutukar biyan basussukan da suka yi mata katutu.
Sai dai janye tallafin da kuma kara harajin da gwamnatin kasar ta yi a ’yan kwanakin nan ya dada ta’azzara tsadar rayuwa a kasar, wacce kuma ta sanya jama’a yin zanga-zangar neman sassauci daga gwamnati.
A cewar Kamfanin mai na kasar, gwamnati ta kuma sanya dan kwarya-kwaryar tallafi a kan kananzir da man dizel.
Farashin man fetru dai ya yi tashin gwauron zabi bayan Shugaba Ruto ya janye tallafi. Ya kuma dada tashi a watan Yuli bayan gwamnatin ta kara kudaden harajin man da sauran kayayyakin makamasji a kasar.