✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KEDCO ya fara raba mitocin wutar lantarki kyauta a Kano

Kamfanin KEDCO na ya fara raba wa kwastomomi 87,747 mitocin wutar lantarki kyauta

Kamfanin rarraba watar lantarki na Kano (KEDCO), ya kaddamar da rarraba mitocin wutar lantarki guda 87,747, kyauta a Jihar Kano.

Shugaban KEDCO, Jamil Isyaku Gwamna, ya kaddamar da rabon ne bayan umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi na rarraba mita miliyan shida ga kwastomomi a fadin Najeriya.

Gwamna, ya samu wakilcin Babban Jami’in Kula da Ayyukan kamfanin, Vijay Sonawane, a wurin taron rarraba mitocin kyauta ga kwastomomin da basu taba karbar takardar shaidar biyan kudin wutar lantarki ba.

“Raba mita kyauta ga kwastomomin da ba su taba karbar takardar shaidar biyan kudin wutar lantarki ba kafin wannan lokacin,” Kamar yadda ya fada.

Gwamna, ya gargadi kwastomomi su guji lalata mitar ko wasarere da ita ta hanyar da bata dace ba, kuma duk wanda aka kama da aikata wani abu na laifi da mitar za a hukunta shi.

A nasa jawabin, Shugaban Sashen Kula da Kwastomomi, Abubakar Yusuf, ya ce suna da akalla kwastomomi miliyan daya a jihohin Kano da Katsina da Jigawa wanda aka sa ran za su samu mitar kyauta.

Ya yi kira ga kwastomomin da su yi amfani da mitar kamar yadda ya dace.

“Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 a Najeriya sun tanadi mita miliyan shida da za su raba wa kwastomominsu.

“Muna da akalla kwastomomi miliyan daya a jihohin Kano da Katsina da Jigawa da muke sa ran za su samu mitarsu kyauta nan da dan kankanin lokaci.

“Ba abu ne da za a saka rai da shi ba a rana daya ko sati ko wata ba amma dai tuntuni an fara rabawa”, kamar yadda ya fada.