✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kayan Sallah: Dandalin sada zumunta ya tallafa wa marayu 100 a Kano

Zauren da ke kan manhajar WhatsApp ya tallafa wa marayu 100 da kayan Sallah a Kano.

Wani zauren sada zumunta a kan manhajar WhatsApp ya tallafa wa marayu 100 da kayan Sallah a Kano.

Dandalin wanda tun farko aka kirkira don taimakon kai da kai da marasa galihu, ya fadada tallafin nasa ne zuwa ga marayu da mata gwagware.

Shugabar Dandalin, wacce kuma ta kafa shi, Fatima Zahra Galadima, ta ce mambobin zauren sun yi karo-karo ne suka sayi kayan tallafin da suka raba wa marayu 100 a Kano.

Zahra Galadima, ta ce kafin kayan sallah, sun raba wa marayu kayan azumi don samun ladar ciyarwa a watan Ramadan da kuma falalar ciyar da mubakata, musamman marayu.

“Zauren Sada Zumunta na Manhajar WhatsApp ya saba gudanar da ayyykan alkhairi ba sai watan azumi ba, ko a kwanakin baya sun gudanar da wani taro a Zariya inda suka tallafa wa gajiyayyu,” inji ta.

Ta ce sun tallafa wa matan ne saboda yawancinsu iyayen marayu ne kuma ba su da mataimaka.

A cewarta, tallafin zai taimaka wa matan su samun sana’a da za su lallaba domin dogaro da kansu da rage wasu matsalolin rayuwa.

Daga nan sai ta yi kira ga masu hannu da shuni da gwamnati da su rika tallafa wa irin wadannan mata da marayu.