Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili da fata Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan kayan hadin soyayyar ma’aurata. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin:
Sinadari na hudu cikin kayan hadin gina ingantacciyar soyayya shi ne ladubban magana, hira, zance da kuma sadarwa tsakanin ma’aurata.
Muhimman abubuwa:
*Yana da matukar muhimmanci ga ma’aurata su rika zabar kalmomi mafiya dadi, mafiya dacewa da kowane irin zancen da suke yi.
*Haka kuma yawan yaba wa juna shi ma abu ne mai muhimmanci wajen rayar da shukar soyayya a zuciyar ma’aurata, sai ma’aurata su rika haka ko da sau daya ne a kullum, kuma yabo na gaskiya ba na riya ba. Sai a lura da wani abu na musamman a yabi wanda ake aure da shi; kuma ya kasance ana dan caccanja abin yabon ba kullum a kama abu daya a yi ta maimaita yabo a kai ba.
*Sannan a rika yabon wanda ake aure a gaban wadansu daban wadanda za su iya sanar da shi wannan yabo, kamar a wajen ’yan uwa.
Sannan ma’aurata su yi kokari su rika fahimtar ra’ayin junansu, kuma su rika yin uzuri ga juna game da ra’ayoyinsu da kalamansu.
Haka kuma ma’aurata su rika kokari suna tauna duk kalamin da zai fito daga bakinsu, don kauce wa fadar kalamin da zai iya haifar da husuma ko jin zafi a tsakaninsu.
Abubuwan kiyayewa:
Ma’aurata su kiyaye fadar kalmomin kushe da kasawa ga junansu; domin irin wadannan kalmomi suna saurin gusar da soyayya da haifar da jin haushin juna a tsakanin ma’aurata.
Sannan ma’aurata su kiyaye takaita surutu lokacin hira, sannan kada daya ya mamaye hirar ya kasance shi kadai ke zuba, ya ki bayar ga dama ga dan uwan aurensa shi ma ya fadi albarkacin bakinsa.
Hirar kyautata soyayya:
Yana da matukar alfanu ga ma’aurata su sanya wani lokaci a kullum, komai kankantarsa, wanda za su rika yin hirar jin dadi da debe kewa a tsakaninsu, yin haka zai yi matukar kyautata so da kaunar da suke wa juna, kuma zai yi matukar inganta dangantakar da ke tsakaninsu. Duk lokacin da suke irin wannan hira, ya kamata ma’aurata su kiyaye da wadannan muhimman abubuwan:
*Ya kasance ma’aurata sun mai da hankalinsu ga juna dari bisa dari, wato su saurari junansu da gaba dayan kafofin hankalinsu.
*Kallo ido cikin ido ya zama wajibi gare su lokacin da suke hirar da kallon fuskar juna da fahimtar sakonnin da ke zayyane a fuskokin junansu wanda zai kara fito da ma’ana da tasirin kalaman da suke fada cikin zuciya da ma’aikatar hankalinsu.
Sauraren yanayin shaukin da ke cakude cikin kowane kalami a lokacin hirar, musamman maigida ya kamata ya kiyaye da wannan, domin mata na da wani irin halin yin magana a murgude, wato su fadi magana alhali a cikin zuciyarsu ba hakan suke nufi ba, ta hanyar sauraren shaukin da ya cakudu da kalamin, ko yanayin zane, launi da shimfidar fuska, ko yanayin sarrafa jiki ne kadai zai sa a fahimci zurfi da ainihin furucin da suka yi.
*Ma’aurata su kasance masu lura da yanayin harshen junansu lokacin hirar, wannan zai kara kusanci da jin dadin hirar ga ma’aurata.
Sannan ma’aurata su lura kada su rika katse junansu yayin irin wannan hira, duk wanda yake wata magana, komai rashin muhimmancinta a wajen mai sauraren, ya yi hakuri ya bar shi sai ya kai aya, domin katse mutum lokacin da yake tsakiyar zance na haifar da jin haushi cikin zuciyar wanda aka katse din. Yana da matukar alfanu kowane daga cikin ma’aurata a ba shi cikakkiyar dama ya fadi duk abin da ke ransa, kuma a saurare shi cikakken sauraro.
Sai mako na gaba insha Allah da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.
WASIKU