Su ce amfani da wadannan magunguna za su sa su ga darajar da yake ba su ta karu. Zai mayar da su ‘yan gaban goshinsa; zai mayar da su sun fi nono fari; zai mayar da su sun fi zuma zaki; zai kumaa mayar da su sun fi kamshin almiski kamshi.
Ire-iren wadannan kalamai sai ya sa ka ga wasu matan sun fara amfani da kayan da’a.
(6) Shirin iyaye mata: Wasu matan kan yi amfani da kayan da’a sakamakon shawara daga iyaye mata ko shirin iyaye mata. Inda wasu iyayen duk lokacin da ‘yarsu za ta yi aure, sai sun shirya ta, wato su dafa ta, ta hanyar yin jike-jike da shaye-shaye da shafe-shafe da kuma yin turare-turare da kayan da’a. Wani lokaci za ka samu har bayan aure ma iyaye mata za su ci gaba da dafa ‘ya’yan nasu.
Ka ji suna cewa da ‘ya’yan su, “ Yanzu ba a zama haka, domin idan kika tsaya, kina ji, kina kuma gani sai kwado ya yi miki kafa, don haka za mu shirya ki yadda zai mayar da ke ‘yar lelensa”. A jika wannan, a kuma shafa wancan.
(6) Kishi: Wasu matan na amfani da kayan da’a don son fita daban daga sauran mata, musamman ma idan mijin yana da mata sama da daya. Wannan sai ya sanya su shiga amfani da kayan da’a duk don mijin ya ba su wani fifiko da daraja daga cikin matansa. Don kuma idan ranar kwanansu ne, mazajen nasu suna turmitsitsi da tururuwa kamar ana ingiza keyar su izuwa gare su, kasancewar mazajen nasu sun san sun fita daban da sauran matansu.
(7) Gani da jin kawaye na amfani da kayan da’a: Wani lokaci mata idan sun zauna suna hirar yadda al’amuran duniyar rayuwar aurensu take garawa, ciki kuwa har da yadda suke gudanar da kwanciyar aure, ta hanyar fallasar da matakan da kuma shirye-shiryen da suke wa mazajensu. Sakamakon labarta gardi da kuma aikin da kayan da’a suke yi yayin gabatar da kwanciyar aure, sai wasu matan da ba sa amfani da kayan da’a, sai su shiga amfani da su, a zuwan su ma su ji abin da ake ji, ko kuma su burge mijinsu, ko dai su samu daraja da daukaka a wajen mazajensu.
ILLOLIN KAYAN dA’A GA LAFIYA.
Sakamakon ziyarce-ziyarcen zuwa asibitoci hade da kuma tambayar wadanda abin ya shafa kai-tsaye da kuma sauran nazarce-nazarce da bin diddigi da na yi, sai na fahimci cewa, amfani da kayan da’a na da illoli ga lafiyar wadanda suke amfani da su. Illolin sun hada da:
(1) kaikayin Gaba: Sakamakon amfani da kayan da’a, musammman ma na Matsawa da na Turare da wasu matan kan yi, sai hakan ya haifar musu da kaikayin gaba. Sukan matsa ko saka sinadarin kayan da’a a al’aurarsu, ko kuma turara al’aurar tasu, wanda a karshe maimakon hakar ta cimma ruwa, ta hanyar samun biyan bukata, sai cibi ya zama kari ta hanyar samuwar kaikayin gaba. Wanda idan suka zauna ba abin da za ka ga su na yi face sose-soshe. Hakan ba karamin ci-musu-tuwo-a-kwarya yake ba.
(2) Zubar Ruwa Daga Al’aura: Sakamakon amfani da kayan da’a na matsi da na turare, sai ya haifar wa wasu matan zubar ruwa mai doyi daga al’aurarsu. Wanda duk wajen da suka zauna, bayan sun tashi sai ka ga wajen ya baci, ko kuma ka ji wurin ya gume da wari mai tayar da hankali. Ba su da wani aiki face wanka da wanki. Akwai wacce na tarar ta na kuka a asibiti, bayan na tambaye ta dalilin kukanta, sai ta sanar da ni, sakamakon amfani da kayan da’a, wanda ya yi sanadiyyar zubar ruwa mai wari a gabanta, sai mijin ta ya daina kwanciyar aure da ita, ya daina hada kwanciya da ita, ya kuma daina cin abincin da ta girka. Cikin kuka ta ci gaba da sanar da ni, abin ya zame mata goma da gomiya, wato bayan mijin ya yi shakulatin-bangaro da ita, sai kuma ya je ya karo aure.
(3) Shanyewar Jiki: Sakamakon amfani da kayan da’a wanda ya kunshi na shaye-shaye da shafe-shafe, sai hakan ya janyo wa wasu matan shanyewar jiki. kiri-kiri suna gani mijin nasu ya kara aure, ba kuma wani abu da za su iya.
(4) barin Ciki: Amfani da kayan da’a, wanda ya kunshi na matsawa ko sanyawa a cikin al’aura ko na shaye-shaye yana janyo zubewar ciki. Musamman ma na matsawa ko na sanyawa, misali, sanya Yashin Madina a cikin al’aura, wanda yake shiga cikin al’aura har zuwa mahaifa, idan har ciki ya shiga to sinadaran Yashin Madina sukan cakudu da kwkyayen mahaifa, karshe dai su lalata cikin.