✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kawo karshen rikici a kan iyakar Binuwai da Nasarawa

A kwanakin baya ne gwamnonin jihohin Nasarawa da Binuwai suka sake yunkuri don kawo karshen mummunan rikicin da ke faruwa a tsakani Fulani makiyaya a…

A kwanakin baya ne gwamnonin jihohin Nasarawa da Binuwai suka sake yunkuri don kawo karshen mummunan rikicin da ke faruwa a tsakani Fulani makiyaya a bangaren Nasarawa da kuma ’yan kabilar Tibi a bangaren Jihar Binuwai.
Ganawar ta biyo bayan sake barkewar rikici ne a tsakanin al’ummomin biyu a farkon watan jiya, inda ya ci rayukan jama’a a bangarorin biyu.
Gwamna Gabriel Suswam na Jihar Binuwai da Gwamna Tanko Al-Makura na Nasarawa sun gana ne a Makurdi, fadar Jihar Benuwai, a makon jiya don nemo maganin matsalar da take kawo damuwa da tsoro ga al’ummomi da dama a jihohin biyu.
Galibi matsalar tana aukuwa ne kan batun wurin kiwo a bangaren Jihar Nasarawa da ke da albarkar wurin kiwo, wadda ke iya zama tattalin arzikin da wani kan dogara da shi a daya bangaren da ke iya jawo takaddama da sauran.
Yunkurin baya don kawo karshen matsalar cikin ruwan sanyi ya kasa cimma nasara. Kuma lokacin da rikicin na baya-bayan nan ya barke ’yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun bukaci a ajiye jami’an tsaro na dindindin a yankunan da ake rikici da ke kan iyakokin jihohin domin hana sake aukuwar wani rikici.  
A taronsu, gwamnonin sun amince su ‘karfafa tsaro’ domin hana duk wani yunkurin barkewar yakin kabilanci da rikicin ka iya haifarwa.
Kuma sun amince su gano hanyoyi da maboyar masu aikata miyagun ayyuka da masu tallafa musu da suke amfani da rashin fahimtar juna a tsakanin manoma da makiyayan suna tayar da hankali domin bukatun kansu.
Gwamna Suswam ya kausasa a zarginsa cewa wasu al’ummu a bangaren iyakar Jihar Nasarawa suna sane da ayyukan makiyayan har suna ba su kariya a duk lokacin da suka dawo daga kai hari kan jama’ar Jihar Binuwai.
“An kai mutanenmu bango, wannan shi ne dalilin da ya sa ba za mu kyale wannan kisa da lalata dukiya na rashin imani su ci gaba ba,” Suswan ya fada a taronsu da Al-Makura.
A nasa bangaren Gwamnan Nasarawa ya nuna damuwa kan lamarin da ya faru a baya inda wasu makiyaya suka kai hari ga wasu jama’ar Jihar Binuwai, kuma ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da hada hannu da takwararta ta Jihara Binuwai domin kawo karshen rikicin.
“Za mu yi iyakar kokarinmu wajen kawo karshen wannan rikici saboda mun yi alkawarin kare rayuwa da dukiyar jama’armu,” inji shi.
daya daga cikin matakan da ya ba da sanarwar fara dauka, daga yanzu za a dora alhakin sake aukuwar rikici kan sarakunan yankin da rikicin ya balle.
karfafa kyakkyawar dangantaka a tsakanin jama’ar da suke kan iyakokin jihohin biyu yana da muhimmanci wajen magance rikicin kabilancin.
Wannan hanya za ta taimaka ga jihohin Binuwai da Nasarawa idan Fulani makiyaya da Tibi manoma za su bullo da wata hanyar karfafa dangataka a tsakaninsu ta ganawa a kullum. Wannan zai samu ta hanyar wayar da kai a tsakanin al’ummomin biyu.
Kuma a duba batun kara tura ’yan sanda domin su taimaka wajen tabbatar da bin doka tare da dakile miyagun ayyukan da suke haifar da rikicin yana da muhimmanci.
Sannan bai kamata a dauki laifin da wani makiyayi ya yi shi kadai a dora a kan daukacin al’ummarsa ba, wanda galibi hakan ke haddasa bazuwar rikici.
Kuma dora wa masu unguwanni da hakimai das aura shugabannin al’umma alhakin laifin wasu kalilan abin shakku ne. Ana iya bukatar su lallashi jama’arsu su kai rahoton halayen wadanda suke ganin suna iya jawo tashin hankali.
Bai kamata mahukuntan Jihar Binuwai su zauna suna jiran ganin matakin da Jihar Nasarawa za ta dauka ba, suna da rawar takawa wajen jawo hankalin jama’arsu da ke kan iyaka su kai rahoton yi musu ba daidai ba ga sarakuna da hukumomin tsaro maimakon su dauki doka a hannunsu.