✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kauraye sun kashe matashi kan waya a KKatsina

Da yammacin Talatar da ta gabata, wadansu matasa da ake zargin kauraye ne suka kashe wani matashi mai suna Abdullahi Muhammad Madugu, dan shekara 18,…

Da yammacin Talatar da ta gabata, wadansu matasa da ake zargin kauraye ne suka kashe wani matashi mai suna Abdullahi Muhammad Madugu, dan shekara 18, wanda bai dade da kammala makaranta ba.
Matashin wanda aka kashe a kofar gidansu da ke Unguwar Inwala bayan makarantar ATC, kan titin kofar kwaya, a birnin Katsina, mahaifinsa Alhaji Muhammad Rumbun Hatsi ya ce, dansa na zaune a bakin rijiya da abokansa suna hira, lokacin da gungun matasan dauke da makamai suka iske su. Ya ce ganin haka ya sa suka tsorata, kowa ya yi ta kansa; a lokacin da shi ya nufo gida da nufin tsira da rayuwarsa. Amma kaurayen suka biyo shhi, domin kwatar wayar salular da ke hannunsa wadda ke da ’yar tsada.
“Yaron ya zo bakin kofar gida ne, sai wani daga cikinsu ya sare shi da makami a wuya, inda babbar jijiyar wuyar ta datse, nan take ya fadi, su kuma suka yi awon gaba da wayar,” inji mahaifin mamacin.
Ya ci gaba da cewa: “Ba a dauki lokaci ba ya ce ga garinku nan. Shi kuma daya yaron da suka raunata, mai suna Mansir Lawal yana samun sauki. Wannan hari na kaurayen yana ba mu mamaki, saboda kusan dukkansu ’yan cikin unguwar nan ne.”
Ita dai wannan unguwa ta Inwala ta yi kaurin suna a garin na Katsina a batun kauranci saboda har ta kai fagen mutun ba zai iya wucewa a cikinta ba da zarar an ce an gama Sallar Isha’i. Wasu lokuta ma da rana-tsaka za a tare mutun a karbe masa kudi ko wayar hannu. Idan an samu gardama su sari mutun da makami ko su fizge abin da ke hannun mutum.
Kamar yadda Aminiya ta ji daga bakin mutane, matasan unguwar sun yi suna a kan kai wa jama’a hari da makami a sassa daban-daban na cikin garin. Kamar yadda wani wanda bai son a ambaci sunansa ya ce: “Babban abin da ya fi ba mu mamaki shi ne, su dai matasan nan a gaban iyayensu wadansu ma har da kakanninsu a cikin unguwar suke aiwatar da wannan ta’asa amma har zuwa yau babu wani matakin da suke dauka. Wasu lokutan ma sukan yi musun a ce ’ya’yansu ne, bayan kuma sun san hakan. Wani abin kuma da yake kara daure mana kai shi ne, tamkar babu jami’an tsaro a garin. Wani abin ban haushin shi ne, koda an yi wani abu aka je aka kama wadansu, da wuya a kwana biyu ba ka ga an sako masu laifin ba. Kusan yanzu a cikin garin Katsina, da wuya ka ji an kai harin kauraye ba tare da ’yan wannan unguwa ta Inwala ba.”
Tuni dai jami’ in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Salisu Abubakar Agaisa ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce har jami’ansu sun kamo wadansu daga cikin wadanda ake zargi da wannan aika-aika. Daga cikin wadanda aka kama har da wadanda suka yi kaurin suna a kan wadannan hare-hare. Matasan da aka kama sun hada da Rangandu da Sagna da Kurgu da sauransu kuma suna ba jami’an bayanan da za su sanya a kama hakikanin wanda ya yi sarar da ta yi sanadiyar mutuwar Abdullahi saboda wayar salula.
Kakakin na ’yan sanda ya  yi kira ga jama’a su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai tare da gaggawar kai rahoton duk wani abin da ba su amince da shi ba, domin ba jami’an samun damar daukar matakan da suka dace a cikin lokaci.