✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsina Polo Kulob ta yi wasa don karrama ’ya’yanta

A makon jiya ne kungiyar wasan kwallon dawaki ta Katsina ta shirya wani wasa na cikin gida, domin taya murna da kuma karrama wasu ’ya’ynta…

A makon jiya ne kungiyar wasan kwallon dawaki ta Katsina ta shirya wani wasa na cikin gida, domin taya murna da kuma karrama wasu ’ya’ynta hudu da suka samu wasu mukamai a masarauta da kuma gwamnati.

A makon da ya gabata ne mai martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmumini Kabir Usman ya yi wasu nade-nade a fadarsa, wadanda daga cikinsu har da Hakimi guda, wanda kuma dan wasan polon ne na kungiyar tare da wasu ’yan wasa uku.

Wadanda sarkin ya nada sun hada da Sarkin Fulani Dambo, Hakimin Ingawa Alhaji Tukur Sule Abubukar, sai Alhaji Hassan Kabir Usman Nagogo da ya samu Sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida na (I), tare da Alhaji Sama’ila Kabir Usman Nagogo a kan Sarautar Mainan Katsina na farko, sai Wazirin Dokan Katsina Dokta Aminu Waziri. Sai kuma wanda ya samu mukami daga Gwamnatin Katsina shi ne Madawakin Majidadi, Alhaji Sani Lawal Bakin Kasuwa; wanda ya samu mukamin Babban Mataimakin Babban Akanta na Jihar Katsina. Bisa wannan matsayin da ’yan kungiyar suka samu ne aka shirya wannan wasa na cikin gida. An kuma fitar da bangarori biyu, bangaren Maina da kuma na DAG.

An buga wasan a filin wasan Polo na Sa Usman Nagogo da ke Kofar ’Yandaka. An tashi wasan kowa na da ci uku.

Daga cikin wadanda suka je wajen wannan wasa har da shugaban kungiyar na Mahadi Ka  Ture, Danmadamin Katsina Alhaji Usman Nagogo da Sarkin Pauwan Katsina, Alhaji Yusuf Lawal Kankara da Shugaban kungiyar, Bunun Katsina, Alhaji Salisu Ado Shinkafi, Galadiman Fardami Alhaji Husaini Saminu Darma, sai mai baiyawa kungiyar shawara ta fuskar shari’a Barista Abdu Ladan Kofar Soro da Mataimakin Darakta a ma’aikatar ilmi ta Jaha Alhaji Amadu Abubakar Unguwar Yari da sauran manyan baki.

Irin wannan wasan karramawa dai, Marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko wanda ya kawo wasan daga Ingila aka fara yi wa irinsa a can kasar ta Ingila, a shekarar 1930; don nuna farin ciki a kan yadda ya kawo wasan. Sai kuma Marigayi Sarkin Katsina Sa Usman Nagogo, wanda aka yi wa irinsa har sau biyu a can dai kasar ta Ingila. Na farko kasancewarsa kwararre a wasan, bayan amsa gayyatar Turawa da yake yi don buga wasan. Sai kuma girma da ya samu ta fuskar wasan, domin shi ne mutum na farko da ya samu (+7)a wasan. Bayan shi, sai Magariyi Sarkin Katsina Dokta Alhaji Muhammadu Kabir Usman, a lokacin da aka nada shi Sarki. Sai Sarki mai ci yanzu, Dokta Abdulmumini Kabir Usman.