Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ile-Tuntun a jihar Oyo ta raba wani aure mai shekara uku kan zargin uban mijin da yiyin katsa-landan a cikin auren.
A ranar Talata kotun ta kashe aure tsakanin Amosun Babatunde da Ibukun mai zargin surukinta da hure wa mjinta kunne ya juya mata baya.
“Kafin aurenmu da Babatunde sai da na samu aiki a Legas kuma muka yi yarjejeniyar zan ci gaba idan muka yi aure.
“Amma bayan yin auren namu sai ya ce sam bai san da maganar ba, sai dai na hakura na zauna a gida.
“Ni kuma na ki yarda. Amma duk lokacin da ya ziyarci iyayensa sai su sauya masa tunani, suka kuma kauracewa duk wani yunkurin yin sulhu”, inji Ibukun.
Shi kuwa mijin cewa ya yi yana da dalilin neman a warware igiyar auren nasu.
Yayin zaman kotun na farko dai, mahaifin Babatunden, Johnson ya bayar da shaida a gaban kotun saboda dan nasa baya nan.
A cewarsa, “Ya mai shari’a, ban taba ce wa dana ya juya mata baya ba. Ba ta da hali mai kyau.
“Lokacin tana karatu da gangan ta ki yarda ta dauki ciki har sai da ta gama yi wa kasa hidima.
“A nawa tunanin, kamata ya yi ma’aurata su rayu har abada, amma a kullum mahaifiyarta ce take daure mata gindi.
“Bugu da kari, ba ta yin shigar mutunci irinta matan aure, kullum sai dai ta rika matsatstsun kaya”, inji shi.
Ita ma da ta ke bayar da tata shaidar, mahaifiyar Amosun ta ce kamata ya yi mahaifin Babatunde ya kyale ma’auratan su sasanta tsakaninsu ba tare da tsoma musu baki ba.
Da ya ke yanke hukuncin, Mai Shari’a Henry Agbaje ya ce kotun ta yanke shawarar datse igiyar auren ne saboda a samu zaman lafiya tare da shawartar ma’auratan da su kaurace wa duk wata karan-batta a nan gaba.