Kalaman danjuma kira ne ga tayar da zaune-tsaye
Katobarar da tsohon Hafsan Hasoshin Sojin Najeriya kuma tsohon Ministan Tsaro, Laftana Janar Theophilus Yakubu Danjuma ya yi cewa sojojin Najeriya suna hada baki da ’yan bindiga wajen kashe mutane inda ya bukaci jama’a su tashi su kare kawunansu daga abin da ya kira yunkurin shafe su ta jawo cece-ku-ce a kasar nan.
A ranar Asabar da ta gabata ce, Janar T. Y. danjuma ya yi wannan katobara a wajen bikin yaye daliban Jami’ar Jihar Taraba da aka gudanar a Jalingo fadar jihar, inda ya zargi sojojin da taimaka wa ’yan bindiga suna kai hare-hare a kan wasu kabilu a sassan kasar nan, ya ce idan aka ci gaba da kai irin wadannan hare-hare, abin da yake faruwa a Somaliya zai kasance wasan yara idan aka kwatanta da abin da zai faru a Najeriya.
Janar danjuma ya ce bai kamata jama’ar kasar nan su dogara da sojoji wajen samar musu da tsaro ba, inda ya shawarci jama’a su kare kawunansu ko kuma su hadu da kisan kare-dangi.
Janar danjuma ya ce: “Sojoji ba ’yan ba-ruwanmu ba ne, suna taimaka wa ’yan bindiga da suke kashe mutane suke kashe ’yan Najeriya. Su suke yi musu rakiya suna ba su kariya. Don idan kuna dogaro da sojoji don su hana kashe-kashen za ku mutu daya bayan daya.”
Sai ya yi barazanar cewa idan ba a dakatar da kashe-kashe a jiharsa da sauran garuruwan Najeriya ba, to rikici zai balle a kasar nan.
“Wajibi ne a dakatar da kisan shafe kabilu a Jihar Taraba. Wajibi ne a dakatar a duk sassan Najeriya ko kuma abin da yake faruwa a Somaliya ya zama wasan yara. Ina kiran kowannenku ya zauna cikin shiri kuma ko kare kasarku ku kare yankunanku ku kare jiharku. Ba ku da inda za ku je,” inji shi.
Kalaman danjuma kira ne ga tayar da zaune-tsaye – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta bayyana kalaman na Janar danjuma da kiran a tayar da zaune-tsaye. Ministan Tsaro, Mansur dan Ali wanda ya mayar da martani ga Janar danjuma ya ce, “Rundunar Sojin Najeriya kintsattsiyar cibiya ce da take da cikakkiyar kwarewa wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda tsarin mulki ya dora mata.”
Ministan wanda ya fitar da wata sanarwa ta hannun Kakakinsa Kanar Tukur Gusau ya ce, duk wanda yake da wata shaida ta aikata ba daidai ba ko nuna sakaci da aiki daga wani soja ya kawo ta hanyar da ta dace don daukar mataki.
Ministan ya nuna takaici kan yadda babban mutum irin danjuma zai fito yana zargin cewa sojoji suna hada baki da ’yan bindiga don haka mutane su tashi su kare kansu, inda ya ce: “Wannan babban abin bakin ciki ne kuma tunzura mutane ne su tayar da zaune-tsaye da bai kamata masu fatan alheri ga kasar nan su saurare shi ba.”
Kalamansa abin takaici ne – Sojoji
A martanin da Rundunar Sojin Najeriya ta mayar ta bakin Kakakinta Birgediya Janar Tedas Chukwu ta nuna takaici kan kalaman na Janar danjuma wadda ta ce sun zo ne a daidai lokacin da sojoji suka fara kokarin raba jama’a da makamai a yankin Arewa ta Tsakiya.
Sanarwar sojin wadda ta ce ba tana son musayar yawu da danjuma ba ne, ta ce to amma wajibi ne ta bayyana hakikanin gaskiya don amfanin al’ummar Jihar Taraba da na Najeriya baki daya.
Sojojin sun kuma zargi Gwamnatin Jihar Taraba da kin ba su hadin kai a kokarin da suke yi wajen magance rikicin makiyaya da manoma a jihar a karkashin shirinsu na AYEM AKPATUMA, saboda sojojin sun tsaya kai-da-fata kan ba za su goyi bayan kowane bangare ba.
“Sanannen abu ne cewa a lokacin da aka kaddamar da shirin AYEM AKPATUMA, Gwamnatin Jihar Taraba ta ki hada kai da sojoji saboda tsayawar sojojin kai-da-fata cewa za su kasance marasa goyon bayan kowane bangare a rikicin na makiyaya da manoma. Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da kasancewa haka. Kuma Rundunar Sojin Najeriya tana shawartar al’ummar Jihar Taraba da sauran ’yan Najeriya su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum tare da kiyaye doka da oda, kuma duk wanda aka kama da bindiga ko harsashi zai yaba wa aya zakinta kamar yadda dokar kasa ta tanada. Duk wani dan kasa mai kiyaye doka da oda za a tabbatar da ba shi kariya ba tare da nuna bambanci ba wajen kare rayuwarsa da dukiyarsa,” inji sojojin.
Sanatoci sun dakatar da muhawara kan zargin danjuma
Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara a kan zargin da Janar danjuma ya yi cewa sojoji suna hada baki da ’yan bindiga wajen yin kashe-kashe. A ranar Talata ce majalisar ta yanke shawarar za ta yi muhawara kan zargin bayan da Sanata Yusuf A. Yusuf na APC daga Taraba ya jawo hankalinta game da zargin.
Majalisar ta dakatar da muhawarar ce shekaranjiya Laraba saboda zafin da harkoki suka yi kan lamarin. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa “Saboda ba mu son zafafa harkokin siyasa ne, domin tsohon Janar din da sojoji sun zafafa lamarin don haka muka dakatar.”