A yayin da ’yan Najeriya ke rige-rigen yin rajistar katin shaidar dan kasa, ma’aikatan Hukumar NIMC mai kula da yin rajistsar sun tsunduma yajin aiki.
Ma’aikatan na NIMC sun fara yajin aikin ne a safiyar ranar Alhamis, yayin da wa’adin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na rufe layukan wayan da ba a yi musu rajista da lambar dan kasa (NIN) ba ke kara matsowa.
- Miji ya tsere bayan Matarsa ta haifi ’Yan hudu
- Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja
- An yanke wa karamar yarinya al’aura a Bauchi
- Amurka: Trump ya amince ya mika wa Biden mulki
Kungiyar ma’aikatan ta ce, “Kwamitin Zartarwa Reshen NIMCI na umartar ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa a Hedikwata da rasssan Jihohi da su yi zamansu a gida daga yau 7 ga Janairu 2021, kar su yi aikin komai.
“Muna kuma shawarta mutane da su kaurace wa ofisoshin NIMC na kananan hukumomi da sauran cibiyoyi domin jami’an kwamitin aiki da cikawa za su zaga domin tabbatar da wannan umarni,” inji sanarwar da Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN) Reshen NIMC, Asekokhai Lucky Michael da Sakatarensa, Odia Victor suka fitar.
Ma’aikatan sun dauki matakin ne domin tabbatar biyan bukatunsu da suka hada da kariyarsu daga cutar COVID-19 da kuma biyan su sabon albashi.
Da alama dai yajin aikin zai kawo cikas ga umarnin Gwamnati cewa kowan dan Najeriya ya yi rajisatar lambarsa NIN, ya kuma hada da lambar layin wayarsa.