Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC), reshen Jihar Kano ta cafke ’yan damfara masu cutar mutane da sunan su ma’aikatan hukumar ne.
An cafke ma’aikatan NIMC na bogin ne a samamen da hukumar ta fara don bankado masu yin aikin rajistar shaidar dan kasa na bogi a Jihar.
- Lambar NIN: Za a dakatar da rajista saboda COVID-19 —Minista
- Har yanzu akwai layukan waya miliyan 29 da ba a hada da lambar NIN ba
- Har yanzu akwai layukan waya miliyan 29 da ba a hada da lambar NIN ba
“Mun yi cafke wasu mutane da ke damfarar jama’a da sunan su jami’an NIMC ne.
“A kwanaki uku da muka fara bincike a kwaryar birnin Kano, mun gano shagunan intanet da wasu jami’an bogi masu cutar mutane da sunan hukumarmu,” inji Hukumar.
Ta bayyana a shafinta na Twitter cewa an kama jami’an na bogi dauke da katin shaidar ma’aitan hukumar na bogi, takardun yin rijista mallakar lambar dan kasa (NIN), da sauransu.
Ta ce an mika wadanda ake zargin ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, domin fadada bincike kafin a gurfanar da su a kotu.
NIMC ta gargadi ’yan Najeriya da su yi hattara wajen yin rijistar lambar dan kasa ta NIN saboda kada a damfare su.