✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Katangar makwabci ta kashe yara 3 ’yan gida daya a Gombe

Katangar makwabci ce ta kashe yaran suna barci

Ruwan saman da aka tafka a garin Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe ya sa wani gini ya rushe inda ya danne yara uku ’yan gida daya suna tsaka da barci.

Bayanai sun nuna cewa katangar gidan wani makwabcin gidan ce ta rushe kan gidan, inda ta kashe yaran, sannan ta jikkata wani gudas daya.

Da ake zantawa da mahaifin yaran, Malam Gambo, ya ce a cikin dare ne ruwan sama ya rusa katangar makwabcinsa ta baya, inda ginin ya rushe ya fado kan gidansa ya kashe ’ya’yansa hudu da suke kwance.

Malam Gambo, ya ce lokacin da ya fito zai tafi sallar Asuba sai ya tashi matarsa a kan ta tashi yaran su yi sallar, sai ya wuce masallaci.

Ya ce yana dawowa ya ji tana ta salati, bayan ya tambaye ta abin da ya faru ta shaida masa faruwar lamarin.

Malam Gambo ya ce nan take suka fara kokarin ciro yaran amma suka gagara, sai da suka nemi taimakon makwabta, inda aka samu ciro su sun rasu.

Sai dai ya ce daya yaron da bai rasu ba tuni aka garzaya da shi asibiti inda yake samun kulawa.

Yaran da suka rasu sun hada da Khadija mai shekara 12 da Walida mai shekara 10 da kuma Umaima mai shekara tara.

%d bloggers like this: