✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katafaren koren shinge

Mafi yawancin masu falle shafukan Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya na sane da Katafaren koren shinge da ake baje bayanansa a shafi na babban lauje kowane…

Mafi yawancin masu falle shafukan Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya na sane da Katafaren koren shinge da ake baje bayanansa a shafi na babban lauje kowane mako. Kuma mafi yawanci al’amuran da ake tsokaci a kansu, sun ta’allaka ne game da kwararowar rairayi da zabge kasa da ke kwaranya a jihohin Arewacin kasar nan guda sili da sili. Ni dai na yi sagaraftu da jelen bibiyar ayyukan hukumar Katafaren koren shingen ta kasar Haurobiya, musamman jin cewa, ayyukan da take tsuwurwurtawa sun samo asali ne daga Hukumar Tarairayar kasashen Ifrikiyya.

A watan Noman-Baba na bayar da labarin yadda na yi kai-kawo a tsakanin birnin Dikko da Jihar Zaman-fara, inda na zurma cikin Zurmemen garin Faru da kwarin samfarera. Kuma na gano yadda aka kafa wa wasu tulu ko randunan tara ruwa da ake zukowa daga kwakware mai aikin da makamashin rana. Hakika wasu sun yaba da aikin wannan hukuma, kamar yadda wasu kuwa suka koka da juya akalar aikinsu.
Al’ummar kwarin samfarera sun yi tur da juya akalar randar karfensu da kwakware mai aiki da makamashin rana da aka shirya aiwatarwa a garin, amma kwatsam sai suka ji cewa, an gudanar da aikin a wani kauye da ake kira Kuryar Dembo. Wannan walankewa da aka yi wa al’ummar kwarin-samfarera ta harzuka Babban Barden kwari, har ta kai ga yana kumfar baki. Na lallaba dai na lallashe shi, har ya yi laushi, na kuma ba shi baki, inda na nuna masa cewa, jaridun Dalilin-taron su da Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya duk za su bayyana rashin jin dadinsa, watakila ma hukuma ta dauki matakin gaggawa.
Su kuwa mutanen kauyen Faru da ke cikin karamar Hukumar Zumurmemen gari, sai doki suke yi, musamman ganin cewa an yi musu rundumemiyar ranadar karfe da kwakware mai aiki da makamashin rana, inda dimbin al’umma ke kwankwadar na kwadi; ga kuma tsirrai da itatuwan lambu duk an dasa. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, babban jami’in da ke kula da shingen zurmemen gari a kauyen Faru, ya koka kan cewa, ya shafe watanni babban lauje bai karbi ladar kwadago ba. Domin ko kadago ba a ba shi ba, ballantan ya samu na kwadon mandago.
Haurobiyawa, kuna sane da cewa, ‘ni ma Katafaren Direban Alli ne,’ don haka idan har na gabatar da darasi a kan katafaren koren shinge ban yi laifi ba. Kuma masu yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, sun tabbatar da cewa, ‘wani ma ya yi rawa balle dan makadi.’ Ni dai ba dan mai kidi da ganga ba ne, amma kakana ya kasance babban jami’in kula da gandun daji. Kuma a wancan zamanin ya gudanar da ayyukansa, ya karade birnin Dikko da garuruwan da ke karkashin masarautar, don haka sai mu ci gaba da batu, a cikin kurtu, amma ban da surutu rututu.
A wannan makon da na dawo birnin Haurubja, bayan dogon hutun karshen mako, sai wani Ogana ya bijiro mini da tambayar da aka cillo masa, wai yaya shirin Katafaren koren shinge zai tallafa wajen bunkasa sana’ar na-duke da kiwon bisashe? Game da wannan tambaya da aka bijiro min da ita, na yi wa Ogana alkawarin zan tuntubi wani mashahurin masani don ya fayyace mana yadda za a inganta limbu-limbu a cikin lambu da na-duke tsohon ciniki.
Ni dai abin da na sani, ko an tuntubi masani ko ba a tuntube shi ba, akwai dimbin al’ummar Fullo da ke jelen jalauta jarin nagge da karsana da bijimi a dokar daji. Sannan mafarauta na gararambar harbin gada da barewa da wasu nau’ukan tsuntsaye a kungurmin daji. Babban abin takaici shi ne, ba a yi wa tsuntsaye da dabbobin daji tanadi a daukacin kasafin baje Hauro da aka saba gudanarwa cikin kowace shekara a kasar Haurobiya ba. Uwa-uba, hukumar Katafaren Koren Shinge ba ta taba tunanin fito da wani tsarin kan yadda za a alkinta albarkatun gandun daji ba, ta yadda al’umma za su fahimci muhimmancin giwa da zaki da dan biri mai barna.
Shirin Katafaren koren shinge kamata ya yi a danka shi kacokan a hannun dalibai masu koyon watsatttsake da buda wagagen littattafai a fannin inganta sana’ar na-duke, musamman wadanda ke nazarin gandun daji. Sannan a yi wani hadin gwiwa da mafarauta ko maharba, ta yadda za a hana su harbe-harbe babu kakkautawa a kungurmin daji. Da zarar an samu gungun masu kula da albarkatun gandun daji, to sai hukumar Katafaren koren shinge ta ji da kwararowar rairayi da ke cinye tsirrai da zaftare kasa a dokar daji.
Kula da gandujn daji zai bai wa Haurobiyawa kariya daga hare-haren miyagun ’yan fashi da masu buruntun satar nagge da karsana da bijimi. Sabanin yanzu da aka yi wa dajin rugu rugu-rugu; ga Falgore an yi masa falle-falle, har miyagu na tsalle-tsalle a cikin dare.
Rashin baje kula da gandun daji ta sanya masu haramta bobo da kwambon bokoko suka yi dandazo a saman-bisa; sannan masu fasakwauri kan keta cikin dazuzzuka, don shigo da haramtattun kayayyaki ko kuma kauce wa biyan kudin fito ga hukuma. Batu na ingarman karfen karafa, ana yin aika-aika da tafka ta’asa a kwanon tasar da ke watse cikin dazukan Haurobiya da ma daukacin fadin Ifrikiyya.
Yunkurin kafa katafaren koren shinge zai yi matukar alfanu idan har aka yi hadin gwiwa da Fullo da mafarauta. ’yan Fullo na bukatar a kafa musu makekiyar makiyayar Fullo; su kuwa mafarauta sai a ba su gadin gandun daji; a kuma nusar da su kula da uwar jikin dabbobi da tsirrai. Aiwatar da wannan manufa da makarantarmu ta bijiro da ita, tabbas zai haifar da dimbin alfanu ga al’umma, musamman a wannan lokaci da ake ta kwakwazon kadawar sauyin yanayi, har ta kai ga an gudanar da dandazon mutane a birnin Faris na kasar Faransa karo na karamin lauje da sili.