✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katafaren kanti a Abuja na kin karbar tsoffin kudi

Hukumar kantin ta ce ba ta da masaniyar CBN ya kara wa'adin ci gaba da amfani da tsoffin kudi

Katafaren kantin H-Medix da ke yankin Wuse 2 a Abuja, ya shiga jerin wurare da suka daina karbar tsoffin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1,000.

Daya daga cikin wakilanmu da ya ziyarci kantin ranar Lahadi, ya ga sanarwar a like a kofar shiga.

Sanrwar ta nuna kantin zai daina karbar tsoffin kudin daga ranar Juma’a, 10 ga Fabrairu.

Da wakilinmu ya yi musu tunin kotu ta ba da uamarnin ci gaba da amfanin da tsoffin kudi, daya daga cikin ma’aikatan wurin, ta shaida masa cewa hukumar gudanarwar kantin ta ce ba ta samu sanarwa hakan daga bankunanta ba.

“Hukumar na hada-hadarta ne da bankunan kasuwanci, kuma bankunan ba su ce musu su ci gaba da karbar tsoffin kudin ba kamar yadda suka yi lokacin da aka kara wa’adin zuwa 10 ga Fabrairu.

“Kuma ba mu karanta haka a labarai ba cewa CBN ya kara wa’adin ci gaba da amfani da tsoffin kudin,” in ji ta.

Aminiya ta rawaito yadda wasu mazauna Abuja ke bijire wa karbar tsoffin kudi duk da kotu ta ba da umarnin ci gaba da amfani da su.