✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar tutar kasar Rasha ta bude a Nijar tun bayan juyin mulki

Sun ce Mutane da dama na zuwa suna neman a dinka musu ita

Teloli a Jamhuriyar Nijar sun ce kasuwar tutar kasar Rasha ta bude a kasar tun bayan juyin mulkin da aka yi wa Mohammed Bazoum a karshen watan Yuli.

A cewar daya daga cikin telolin mai suna Yahaya Oumarou, jama’a da dama a kasar na neman a dinka musu tutar mai launukan fari, shudi da ja, ta hanyar amfani da kekunansu.

Yadda mutanen Nijar ke ta bukatar tutar Rashar ya yi matukar kada hantar kasashen Turawa wadanda ke ganin yunkurin a matsayin wata babbar barazana ga tasirinsu a kasashen na Yammacin Afirka.

“Tun bayan juyin mulkin, na dinka irin wadannan tutocin da dama,” in ji Yahaya, wanda ke sana’ar ɗinkin a Yamai, babban birnin kasar.

Ya kuma ce tutocin kasashen Mali da Burkina Faso da su ma aka fuskanci juyin mulkin a cikinsu a ’yan shekarun nan su ma ana cinikinsu.

Wani mazaunin birnin Yamai, Okocha Abdulaziz, wanda ya shiga zanga-zangar goyon bayan sojoji bayan kifar da gwamnatin ya ce, “Ni mai goyon bayan Rasha ne, dalili ke nan da na zo sayen yadi domin a dinka min tutar.

“Kafin juyin mulkin ban ma san tutar Rasha ba, wannan abin burgewa ne matuka.”

Goyon bayan da Rasha take samu dai ya disashe karsashi da tasirin da kasar Faransa take da shi a fadin Yammacin Afirka.

Gwamnatin sojin. Mali dai ita ma ta juya wa kasar Faransa baya tun lokacin da ta yi juyin mulki a 2021, inda yanzu take hada kai da Rasha wajen yaki da ’yan ta’addan da suka addabi yankin Sahel.

Su ma ’yan kasar Burkina Faso sun rika daga tutar Rasha yayin mummunar zanga-zangar nuna kin jinin Faransa da ta biyo bayan juyin mulkin da aka yi a shekara ta 2022.

(Reuters/NAN)