Tun kafin bude kasuwar hada-hadar ’yan wasan kwallon kafa a nahiyar Turai, an fara hasashe game da makomar wasu fitattun ’yan wasa.
Ya zuwa yanzu dai, akwai wasu ’yan wasa akalla guda 20 da sauya shekarsu ka iya kafa tarihi a bana.
Ana sa ran kasuwar ’yan wasan a Turai za ta kankama da zarar an kammala gasar Euro 2020.
Ga wasu daga cikin ’yan wasan da ake hasashen sauya shekar tasu:
1. Messi: Kwantaragin Lionel Messi, dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, zai kare ranar 30 ga watan Yunin 2021.
Hakan ya sa ake hasashen zai iya sauya sheka.
Kungiyoyin PSG da Manchester City da Juventus na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan, amma sabon shugaban kungiyar ta Barcelona, Joan Laport, na kokarin ganin Messi ya sake sabunta kwantaraginsa da kungiyar.
2. Mbappe: Dan wasan PSG da ke kasar Faransa, kwantaraginsa zai kare a watan Yunin 2022, kuma Real Madrid ta jima tana zawarcinsa.
Kazalika, ana sa ran dan wasan zai yanke hukunci a kan makomarsa da zarar an kammala gasar Euro 2020.
3. Cristiano Ronaldo: Bayan rashin kokari da kungiyar Juventus ta yi a bana har ta gaza lashe gasar Seria A da kuma gasar Zakarun Turai, an fara yada jita-jita cewa Cristiano na neman sabuwar kungiyar da zai koma.
4. Haaland: Haaland ya taka muhimmiyar rawa a bana wajen zura kwallaye da dama a kungiyarsa ta Dortmund.
Hakan ya sa kungiyoyi a nahiyar Turai shiga zawarcinsa.
Chelsea, Real Madrid, Barcelona, Juventus, PSG da Bayern Munich na daga cikin wadanda ke zawarcin dan wasan.
Kwantaraginsa zai kare ne a shekarar 2024 a Dortmund.
5. Griezmann: Bayan shafe shekara biyu a kungiyar Barcelona, dan wasan bai taka wata muhimmiyar rawa ba, lamarin da ya sa kungiyar ta fara tunanin sayar da shi, duk da cewar kwantaraginsa zai kare ne a shekarar 2024.
6. Hazard: Bayan barin Chelsea a 2019, dan wasan ya kasa yin katabus a Real Madrid tsawon shekara biyu sakamakon rauni da yake fama da shi.
Tuni kungiyar ta fara tunanin neman madadinsa.
7. Harry Kane: Dan wasan ya bayyana karara cewar yana son barin Tottenham a bana.
Kane na son komawa wata babbar kungiya inda zai lashe wata babbar gasa, musamman gasar Zakarun Turai.
Manchester City da Chelsea da Manchester United na daga cikin wadanda suke zawarcinsa.
8. Dembele: Barcelona ta sayi Dembele da zummar maye gurbin Neymar a kungiyar, amma dan wasan na fama da rauni.
Kwantaraginsa zai kare a karshen kakar 2022, kuma kungiyar ba ta da niyyar sabuntawa.
Hakan ya sa kungiyar PSG ta fara zawarcin dan wasan.
9. Sergio Ramos: A karshen watan Yunin 2021 kwantaraginsa zai kare da Real Madrid.
Kungiyar ta masa tayin sabon kwantaragi na shekara biyu tare da ragin kashi 10 cikin 100 na albashinsa ko kuma shekara daya ba tare da rage albashi ba, amma dan wasan ya ki amincewa da bukatar ta Madrid.
An dauki tsawon lokaci ana tattaunawa ba tare da cimma matsaya a kan dan wasan ba, wanda hakan ya sa ake tunanin Ramos zai bar kungiyar a kyauta.
10. Donnarumma: Mai tsaron ragar AC Milan Donnarumma, bayan karewar kwantaraginsa, ya ki amincewa ya sake sa-hannu a kungiyar; tuni ya shiga tattaunawa da kungiyar PSG don komawa can.
11. Dybala: Dan wasan mai shekara 27, kuma dan asalin kasar Argentina da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus, ya fara duba yiwuwar barin kungiyar saboda rashin buga wasanni da ya ke yi, kwantaraginsa zai kare a 2022.
12. Bale: Dan wasan ya gama zaman aro a kungiyar Tottenham da ke Ingila daga Real Madrid, ana sa ran zai sake komawa kungiyar tasa, amma wasu rahotanni na bayyana cewar kungiyar na neman kai da shi.
Wasu bayanai kuma na cewar dan wasan na tunanin yin ritaya baki daya daga kwallon kafa.
13. Joao Felix: Dan wasan mai shekara 21 a duniya da ke taka leda a Atletico Madrid na iya barin kungiyar kasancewar ya zama dan wasan benci a kakar wasanni da aka kammala.
Amma akwaii yiwuwar ya ci gaba da zama ya kuma yi fafutuka don tabbatar da gurbinsa a kungiyar.
14. Varane: Kwantaraginsa zai kare a kakar wasanni mai zuwa.
Dan wasan mai shekara 28 a duniya ya lashe manyan gasa a Real Madrid.
Ya bukaci Madrid ta kara masa albashi ko kuma ya bar kungiyar, inda ake sa ran zai koma kungiyar Manchester United.
15. Lautaro: Dan wasan ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa kungiyarsa ta Inter Milan lashe gasar Seria A bayan shekara tara.
Tuni Barcelona da Atletico Madrid da Real Madrid suka shiga zawarcin dan wasan mai shekara 23.
16. Morata: Dan wasan na zaman aro a Juventus, kuma suna da damar sayensa ya zauna dindindin, amma babu tabbacin ko zai ci gaba da zama a kasar Italiya ko zai koma kungiyar Atletico Madrid; kwantaraginsa zai kare a 2023.
17. Sancho: Tun a shekarar da ta wuce kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta matsa lamba kan daukar dan wasan dan asalin Ingila da ke taka leda a Dortmund. Rahotanni sun bayyana cewar dan wasan zai rabbata hannu a Manchester United nan da wasu makonni.
18. Kounde: Bayan nuna bajinta a bana da dan wasan bayan kungiyar Sevilla ya yi, kungiyoyi da dama sun fara zawarcinsa.
19. Depay; Bayan karewar kwantaraginsa da Lyon, ana sa ran dan wasan mai shekaru 27 zai koma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
20. Navas: Mai tsaron ragar PSG din ana sa ran zai koma kungiyar AC Milan, tun bayan da PSG ta shiga tattaunawa da Donnarumma.