✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar da ake hada-hadar naman kare da mushe a Indonesiya

Suna yin hakan tare da sayar da sauran dabbobi kamar jemagu da kyanwoyi da macizai

Wadansu mutane na sacewa tare da kashe dubban karnuka a kauyukan Indonesiya domin sayar da namansu a kasuwannin nama da kayan abinci.

Suna yin hakan tare da sayar da sauran dabbobi kamar jemagu da kyanwoyi da macizai.

Kungiyar Masu Cin naman Kare ta Indonesiya (DMFI), ta wallafa wasu hotuna, bayan sun kama wadanda suke zargin, inda kungiyar ta gano yadda wadansu suke amfani da pincis na karfe wajen kama karnukan, suna daure su kafin jefa su a cikin keji.

Ana iya ganin naman kare da na kyanwa da wasu naman dabbobin daji ciki har da jemagu da macizai masu kama da dabbobin aka samu ana sayarwa a Wuhan na kasar China, wanda ake yi zargin cewa cutar Covid -19 (Kwarona) ta samo asali ne a can.

Musulmin Indonesiya ba sa cin naman kare, amma naman yana da farin jini a yankin Sulawesi, kuma ba shi da tsada.

Ana iya sayen kwanon abinci mai naman kare a kasuwa a kan kudin Indonesiya IDR 25,000 zuwa 35,000 (kimanin Dala 2 ko Naira 831.84.)

Kasuwar hada-hadar naman kare da mushe a Indonesia
Kasuwar hada-hadar naman kare da mushe a Indonesia

Rahoton Hukumar Lafiya na Nahiyar Asiya ya danganta mummunar cutar zomaye ta ‘zoonotic’ da ke yaduwa a cikin garin Sulawesi da cin naman kare.

A Indonesiya, ana safarar karnuka daga nesa zuwa garin Makassar, babban birnin Sulawesi na Kudu, wanda ya kai nisan tafiyar sa’o’i 40 nisan da zai kai mil 1,000.

Shugaban Indonesiya, Joko Widodo yanzu yana fuskantar sabon matsin lamba na rufe kasuwancin naman kare da ake yi a kasar, kamar yadda jaridar mirror.co.uk ta ruwaito.