✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar Alaba da ke Legas ta yi gobara

Babbar kasuwar Alaba da ke yankin Ojo a Jihar Legas ta kama da gobara a ranar Juma'a.

Babbar kasuwar Alaba da ke yankin Ojo a Jihar Legas ta kama da gobara a ranar Juma’a.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas ta ce gobarar ta fara ne daga bacocin da ke kasuwar, ta ci gaba da ci.

Kakakin hukumar Margaret Adeseye ta bayyana cewa gobarar ta fara ne da tsakar dare sakamakon matsalar wutar lantarki.

Ta ce jami’an hukumar na kokarin shawo kan wutar, amm ta nuna damuwa cewa wasu fusatattun mutane sun hana motocin kashe gobara da suka taso daga wasu yanki domin kawo dauki a shawo kan wutar.