✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwanci yana bukatar hakuri da juriya – Alhaji Iliyasu

Alhaji Iliyasu Muhammad da ke Kasuwar ‘Yan Kwalabe a garin Jos babban birnin Jihar Filato, shi ne shugaban kungiyar masu sayar da buhun leda a…

Alhaji Iliyasu Muhammad da ke Kasuwar ‘Yan Kwalabe a garin Jos babban birnin Jihar Filato, shi ne shugaban kungiyar masu sayar da buhun leda a jihar. A wannan tattaunawar da ya yi Aminiya , ya bayyana yadda ya fara harkokin kasuwanci na sayar da buhun leda da irin nasarorin da ya samu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: A wanne lokaci ne ka fara wannan kasuwanci na sayar da buhun leda?

Alhaji Iliyasu: Wannan kasuwanci na sayar da buhuna na fara shi ne, tun kamar shekaru 29 da suka gabata. Farko na fara da sayen buhunan takardar siminti ne. A lokacin na kan je na sayo takardar siminti, a gidajen bulo. Daga nan Jos har Barikin Ladi nake zuwa, domin nemo wadannan buhunan. A haka na rika tafiya, har abin ya fadada na shigo wannan kasuwa ta ’yan kwalabe, a nan garin Jos. Na rika bai wa wasu abokan cikinmu kudade suna tara mani takardar siminti da leda. Idan na tara, sai na dauka na kai wa wasu masu gidanmu a kasuwar katako a nan Jos, na sayar masu.
A haka har Allah Ya sa na zauna a wannan kasuwa har na kai ga wannan matsayi na shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta Jihar Filato.
Aminiya: Kamar ta ya ya kuke gudanar da wannan kasuwanci na buhunan leda?
Alhaji Iliyasu: To shi dai wannan harkoki na kasuwanci buhunan leda mafi yawa mun dogara ne da manoma wajen sayar da buhunan leda. Kashi 70 daga cikin 100 na buhunan ledar da muke sayarwa manoman damina da manoman rani ne suke saya, don zuba kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa. Sannan kuma akwai masu harkokin ma’adanai da suma suke sayen buhunan leda suke zuba ma’adanai da dai sauransu.
Aminiya: Wadanne irin nasarori kake ganin ka cimma a wannan kasuwanci?
Alhaji Iliyasu: To, babu shakka na sami nasarori da dama a wannan kasuwanci na sayar da leda da nake yi, domin akwai mutane da dama da suke karkashina suke cin abinci akalla akwai mutum 30 suke karkashina, a wannan kasuwanci da nake yi.
Haka kuma a halin yanzu, ta dalilin wannan kasuwanci na zama dila a kamfanonin yin buhuna da tabarmi na Royal da ke Kano da kamfanin yin buhuna na Rumbu da ke Kano da kamfanin yin buhuna na Jumbo da ke Kano, da kamfanin yin buhuna na Diamond Super Sack da shi ma yake Kano.
Bayan haka kuma, wata babbar nasarar da nake ganin na cimma kan wannan kasuwanci ita ce a halin yanzu ina bai wa kamfanoni da dama buhuna. Wadannan kamfanoni sun hada da wani kamfanin ma’adanai na mutanen Indiya mai suna Kumar Industry, a Tudun Wada a nan garin Jos.
Sannan akwai kamfanin Jos Foods da kamfanin Lemon kwalaba na Coca Cola. Bayan haka, ina diloli da nake turawa, kaya a Lafiya da ke Jihar Nasarawa da Gombe da Binuwai da kuma Jihar Kaduna da dai sauran wurare.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa ne ya kamata mai wannan kasuwanci ya rike?
Alhaji Iliyasu: To, abubuwan da kowanne kasuwanci yake bukata su ne gaskiya, hakuri da kuma juriya.
Aminiya: A karshe wanne kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati, kan ta taimakawa ’yan kasuwa da sauran masu sana’o’i?
Alhaji Iliyasu: Ni babban kiran da zan yi ga wannan sabuwar gwamnati, ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne a rage wa kamfanoni harajin da ake karba, daga wajensu. Domin rage wa kamfanoni haraji, zai sa a sami saukin kayayyakin da suke sarrafawa. Kuma idan an yi hakan zai isa ga talakawa. Sannan kuma ina kira ga gwamnati, ta rika barin kamfanoni suna zuwa su kawo kayayyakin da za su yi amfani da su, maimakon a ce za a rika bai wa wasu ejan-ejan su kawo daga waje.