Jami’an tsaro a Edo sun cafke wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar da satar mutane.
Wanda ake zargin ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar ne a ranar 1 ga Yuli.
- Ruwan sama zai iya jawo yawan hatsarin jiragen sama a bana – NEMA
- PIB: Majalisa ta amince da dokar man fetur
Wanda ake zargin ya kasance shugaban wata kungiya ta mutum hudu da suka kware wajen garkuwa da mutane, musamman a yankin Bini zuwa Auchi.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin na cikin jerin masu laifuka da rundunar ke nema ruwa a jallo.
An rawaito cewa ya yi garkuwa da wata mata mai suna Lucky Ojezele a yankin Idumwengie da ke kan hanyar Bini zuwa Auchi a ranar 5 ga watan Mayun bana.
Da yake tabbatar da kamun, kakakin ‘yan sandan Jihar Edo, SP Kongtons Bello, ya ce sun cafke mai laifin ne a yankin Aduwawa na birnin na Bini.
A cewarsa, rundunar ‘yan sandan tuni ta cafke daya daga cikin mutanensa sannan ta tura shi zuwa kotu don a yanke masa hukunci.