Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra ta tabbatar da cafke wani mutum mai suna Matthew Nwankwo, wanda ake zargin shugaban wata kungiyar masu garkuwa da mutane ne, shekara bakwai bayan ayyana ana nemansa ruwa a jallo.
Tun a 2015 ne Nwankwo ya tsere lokacin da gwamnatin Anambra ta rushe gidansa da ke kauyen Umuobindo a garin Nteje na Karamar Hukumar Oyi bayan da aka gano yana amfani da gidan a matsayin maboyar mutanen da suka yi garkuwa da su.
- An janye dokar takaita zirga-zirgar Adaidata Sahu a Kano
- Gwamnati Tarayya ta dora alhakin karuwar talauci a kan gwamnoni
‘Yan sanda sun kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar ranar Talata, bayan da jami’an tsaro suka samu bayanan sirri kan maboyarsa.
DSP Toochukwu Ikenga, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da damke wanda ake zargin.
“Wanda ake zargin yana tsare, ana ci gaba da bincike a kansa,” in ji shi.
A cewar kakakin, kasurgumin dan bindigar da yaransa sun addabi jihar da kewayenta wajen fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.