Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta ce nan gaba kadan za ta sanar da karin kudin makaranta a Jami’ar.
Da take tabbatar da cewa za ta kara kudin makarantar, wanda nan gaban kadan za ta sanar, KASU ta karyata labarin da ke yawo na kara kudin makarantar da ya wuce kima.
- Ya auri kanwarsa da ta bace tun tana jaririya
- Yadda harin ’yan bindiga ya tilasta rufe sansanin sojoji a Neja
- Dan majalisa ya halarci zaman Majalisa tsirara
“Hukumar Gudanarwar na kuma jaddada cewa za a yi karin kudi ga kwasa-kwasai, amma ba a sanar ba tukuna.
“Kudaden da ake ta yadawa a kafafen sadar da zumunta ba gaskiya ba ne; Amma nan gaba kadan za a sanar da mutane halin da ake ciki,” inji sanarwar da kakakin Jami’ar, Adamu Nuhu Bargo, ya fitar.
Sai dai sanarwar ta bukaci jama’a su yi watsi da karin kudin da ya zarce kima da ya karade kafafen sadar da zumunta, wanda ya ce kanzon kurege ne.
Tun da farko kafafen sadar da zumunta sun yi ta baza cewa an yi wa daliban karin kudin makaranta da akalla ninki hudu, wasu kuma fiye da hakan.
Bullar labarin karin da aka bayyana cewa ya zarce kima, ya tayar da hankalin dalibai da iyaye, kafin daga baya hukumar Jami’ar ta fito ta karyata, tare da cewa sai nan gaba za ta sanar da karin da aka yi.
“Hukumar Gudanarwar ta kuma tattauna da dalibai a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, 2021, inda ta wayar musu da kai game da tsoron da suke bayyana,” a cewar sanarwar.