✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kashin farko na ’yan Najeriya sun iso Abuja daga Ukraine

Dalibai 451 sun sauka a Abuja da misalin karfe 7:11 na safiya, agogon Najeriya

Jirgin farko na ’yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Poland sakamakon yakin Rasha a Ukraine sun iso Abuja.

Wadanda aka kwaso din sun iso filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin karfe 7:11 na safiyar ranar Juma’a, a jirgin Max Air.

Shugaban Kwamitin Harkokin Waje a Majalisar Wakilai, Yusuf Buba ne ya shaida wa manema labarai cewa dalibai 451 ne suka fara isowa.

Buba na cikin jami’an gwamnati da suka je Bucharest, babban birnin kasar Romania domin kwaso ’yan Najeriya mazauna Ukraine da ke neman dauki.

Ana sa ran za a kwaso kimanin mutum 5,000 da suka guje wa yakin da Rasha a Ukraine.

Yawancinsu sun tsallaka zuwa makwabtan Ukraine da suka hada da Romania, Poland da kuma Hungary da sauransu.

A ranar Alhamis aka sa ran soma kwaso ’yan Najeriyan, sai dai an samu jinkiri saboda wasu dalilai na tsare-tsare da ba su kammala ba.

Cikakken bayani na tafe…