Gwamnatin Jihar Borno ta ce sama da kashi 95 cikin 100 na ainihin masu akidar Boko Haram, musamman wadanda aka kafa kungiyar da su sun mutu ko sun mika wuya.
Mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi mai ritaya ya bayyana haka ne a wata hira da Aminiya a Maiduguri ranar Lahadi.
Ya ce yana kyautata zaton yawancin wadanda aka faro kungiyar da su duk sun mutu, wadanda ke raye a cikinsu ba za su wuci mutum 10 ba.
Abdullahi ya ce, galibin manyan kwamandojin sun mutu ne sakamakon rikicin shugabanci da ya barke tsakanin mayakan kungiyar ISWAP da na Boko Haram masu biyayya ga marigayi Abubakar Shekau, bayan ya rasu a shekarar 2021.
- An kama lakcara kan lalata da dalibansa don ba su maki a Yobe
- HOTUNA: Yadda Aka Gudanar Da Sallar Neman Sauƙin Rayuwa A Zariya
Sauran kuma sojoji ne suka kashe su, sai wadanda suka rasu a sakamakon saran maciji da sauran dalilai.