✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 90 cikin 100 na Dalivan Jami’ar Houdege Cotnou ’yan Najeriya ne

Shugaban Jami’ar Houdege Cotnou’ a Jamhuriyar benin Sa, Majeste dada Awiyan Kokpon Houdegbe, ya bayyana yadda ’yan  Najeriya ke kokarin shiga jami’arsa, har ta kai…

Shugaban Jami’ar Houdege Cotnou’ a Jamhuriyar benin Sa, Majeste dada Awiyan Kokpon Houdegbe, ya bayyana yadda ’yan  Najeriya ke kokarin shiga jami’arsa, har ta kai ga sun fi sauran daliban sauran kasashe yawa.  Ya kuma yi bayanin ne a wajen bikin saukar karatu ta bana, inda jami’ar t ayaye dalibai dubu biyu.

A yayin da yake zantawa da ‘yan jarida jim kadan bayan kammala bikin, mutumin da ya gina wannan makaranta mai zaman kanta Shugaban kungiyar Sarakunan Afrika, Sa, Majeste dada Awiyan Kokpon Houdegbe, cewa ya yi a shekarar da ta wuce jami’ar ta yaye dalibai fiye da dubu 3 ne a yayin da ta yaye dalibai fiye da dubu 2 a shekarar karatu ta bana. 

Ya ce kashi 90 daga cikin 100 na yawan daliban da aka yaye a bara da bana sun fito ne daga Najeriya. Ya ce a duk lokacin da ake gudanar da bikin yaye daliban makarantar, birnin Kotono yana cika makil da mutane ’yan Najeriya ne da suke zuwa domin taya su murna.

Sa Houdegbe ya nuna matukar farin ciki da ganin irin yadda ’yan Najeriya suke rububin neman yin karatu a jami’ar ta HNAU wanda hakan ya karfafa mishi guiwar kara kaimi wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilmi ga matasan Afrika daga wannan makaranta ta yadda matasan daliban da aka yaye a makarantar za suyi gogayya da matasan kasashen duniya da suka ci gaba ta fannin ilmi.

Mukaddashin Shugaban Majalisar dattawan kasar benin Mista Eric Houndete da dakta donald L. bird da wasu sarakunan kasar da baki daga Najeriya da kasashen duniya suna daga cikin manyan mutanen da suka halarci wajen bikin.

Wasu dalibai ’yan Najeriya da ke karatu a Jami’ar Houdegbe North American Unibersity a Jamhuriyar benin sun ce akwai bambancin tsadar karatu a tsakanin kasashen benin da Najeriya. Sun ce malamai ba sa shiga yajin aiki a makarantun kasar benin kamar yadda ake yi a Najeriya. Daliban sun fadi haka ne a zantawarsu da Aminiya a wajen bikin yaye dalibai dubu biyu da Jami’ar Houdegbe ta gudanar a harabar Jami’ar da ke birnin Kotono.

Awal Kabir Muhammed cewa ya yi “a gaskiya Jamia’ar Houdegbe North American Unibersity (HNAU) ta yi rawar gani a kan koyar da dalibai ilmi mai inganci. babu tsadar kudin makaranta a nan kamar yadda ake samu a kasar mu Najeriya kuma ana koya mana darussa da muke fahimtar abubuwan da ake koya mana a tsanake.”

Shi kuwa Abdullahi babangida Jigama ga abin da ya ce “duk da yake akwai makarantu masu yawa a Najeriya, amma akwai matsalolin da suke fuskanta da yake janyo koma bayan ilmi. Daya daga cikin matsalolin ita ce yawan yajin aiki da malaman makarantu ke yi a Najeriya, wanda babu irin haka a nan kasar benin. Kuma wannan jami’a ta (HNAU) babu laifi tana da kyau kwarai kuma akwai saukin biyan kudin makaranta ba kamar yadda ake samun tsadar karatu a makarantun  Najeriya ba. Sannan a cikin aji idan aka koya mana abin da ba mu fahimta ba, sai a dawo a sake yi mana tushi har mu gane komai. Shi ne ya sa na yanke shawarar zuwa yin karatu a nan a maimakon tsayawa a kasata. Ina yin kira ga jami’o’in Najeriya su yi koyi da salon karatu irin na jami’o’in kasar benin.”

Shi ma dalibi Collins Richard cewa ya yi “malaman makarantu a nan Kotono da kasar benin baki daya ba sa yin yajin aiki kamar yadda ake yi a kasarmu Najeriya, wanda yake haifar da dadewar dalibai a cikin makaranta kafin su kammala karatu. Ya kamata makarantun Najeriya su rinka yin irin yadda makarantun benin suke yi wajen koyar da dalibai.”