Rundunar Sojin Sudan ta ce, ta soma kokarin ganin an fitar da jami’an diflomasiya na kasashen Yamma daga cikin kasar a yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Khartoum babban birnin kasar.
Tuni dai Saudiyya da wasu kasashen Yamma suka soma rige-rigen fitar da ’yan kasashensu daga Sudan a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fadan.
- Al-Qaeda ta dauki alhakin kashe Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Mali
- Zababben dan Majalisa mai shekara 36 ya rasu
Shugaban kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce, ya bai wa shugabanin kasashen Amurka da Birtaniya da China da Faransa tabbacin fitar da ’yan kasashensu daga cikin kasar cikin koshin lafiya.
Mutum sama da dari hudu rahotanni ke cewa, sun mutu a kasar, tun bayan barkewar kazamin fada a tsakanin dakarun sojin Sudan na bangaren Shugaban Kasar, Janar al-Burhan da na Shugaban Rundunar RSF wadda Janar Hamdan Dogalo ke jagoranta.
Ya zuwa Juma’ar da gabata dai rahotanni daga Sudan na cewa an samu saukin rikicin da ake ta gwabzawa a cikin ungwannin birnin Khartoum.
Samun saukin na zuwa ne bayan kiraye kirayen tsagaita da aka yi ta yi don samun sukunin gudanar da bikin Salla karama ta karshen watan Ramadan.
Sama da mutane 400 ne aka ruwaito sun mutu, kana dubbai suka jikkata tun da wannan rikici ya barke a ranar Asabar ta makon jiya tsakanin rundunar sojin kasar a karkashin shugaba Abdel Fattah al-Burhan da runduna ta musamman, wanda mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta.
A ranar Juma’a rundunar sojin kasar ta sanar da cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki 3 don bai wa al’ummar kasar damar gudanar da bikin sallah karama, tare da barin kayayyakin agaji su shiga yankunan da ake da bukatar su.
Shaidu daga yankuna da daman a birnin Khartoum sun ce kura ta lafa a Yammacin Juma’a, bayan luguden wuta da aka kwashe kwanaki kusan 7 ana yi a birnin.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce dakarun sojin kasar na fatan ’yan tawayen za su bi dukkan sharuddan tsagaita bude wuta da kuma dakatar da duk wani yunkuri na soji da zai kawo mata cikas.