Kasashe goma sha hudu a duniya sun sanar cewa ranar Asabar za su gudanar da bikin Karamar Sallah a bana.
Hukumomin kasashen sun sanar da cewa Karamar Sallah ta kama ranar Asabar a kasashensu ne saboda ba a samu ganin sabon watan Shawwal ranar Alhamis a kasashen ba.
Kasashen su ne Iran da Libya da Pakistan da Oman da Japan da Malaysia da Indonesia da Brunei da Thailand da Singapore da Australia da kuma Philippines.
A wannan karon dai akasarin kasashen duniya, ciki har da Najeriya da Saudiyya, sun yi Karamar Sallar ne a ranar Juma’a.
Sun yi Karamar Sallah a ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ne bayan a ranar Alhamis 29 ga watan Ramadan, an tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal — na karamar sallah — a kasashen.
Ana yin kamar sallah ne a duk ranar 1 ga watan Shawwal na kalandar Musulunci, mai kwanaki 29 ko 30 a wata, ya danganci lokacin da aka ga jinjirin wata.