✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen da suka karbi bakuncin gasar AFCON a tarihi

Ivory Coast ce za ta karbi bakuncin gasar AFCON a 2023.

A jiya Lahadi ne aka karkare gasar cin Kofin Nahiyyar Afirka wato AFCON 2021, wadda kasar Kamaru ta karbi bakunci.

Karon farko ke nan da tawagar Lion Teranga ta kasar Senegal ta lashe gasar bayan ta samu nasarar doke Masar da ci 4-2 a bugun fanareti a wasan karshen da aka doka a filin wasa na Olembe da ke Yaounde, babban birnin kasar Kamaru, bayan shafe shekaru 60 tana jira.

Wannan ita ce gasar AFCON cikon ta 33 da Hukumar Kwallon Kafar Afirka CAF ke shiryawa duk bayan shekara biyu, inda aka samu akasi ta 2021 ta gudana daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairun 2022.

An shirya gudanar da gasar ce a tsakanin watan Yuni da Yulin bara na 2021, amma tun a ranar 15 ga watan Janairun 2020, Hukumar CAF ta bayar da sanarwar cewa gasar ba za ta gudana ba kamar yadda aka tsara a sakamakon matsalar sauyin yanayi da ka iya shafar ta.

Hakan ce ta sanya CAF ta sanar da cewa za a gudanar da gasar daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga Fabrairun 2021.

Amma daga bisani CAF din ta yi hasashen cewa hakan ma ba zai yiwuwa ba, inda a ranar 30 ga watan Yunin 2020, ta sake dage gasar zuwa Janairun bana a sakamakon radadin da ya biyo bayan annobar coronavirus da ta karya tattalin arzikin duniya.

Sai dai wannan bai sa an sauya lakabin da a bisa tsari za a yi wa gasar ba na AFCON 2021 duk da cewa ta gudana ne a shekarar 2022.

Mai kare kambunta ba ta je ko’ina ba

Kasar Aljeriya wadda ta yi kokarin kare kambunta, tun a zagayen rukuni aka sallame ta, yayin da ita ma kasar Kamaru mai masaukin baki aka kakkabo jirginta a wasan daf da na karshe bayan tawagar Masar ta samu nasarar doke ta a bugun fanareti da wasan ya kai su.

Karo na biyu ke nan da tawagar Lion Teranga ta kasar Senegal ke zuwa wasan karshe na gasar AFCON ba tare da nasara ba, sai a wannan karo, yayin da Masar ta barar da damar daukar kofin a karo na takwas.

Da yake dai lamarin ’yar cude ni in cude ka ce, kuma kowane rabo ba ya ketare mai shi, Senagal wadda ta yi rashin nasara a hannun Aljeriya da ta daga kofin gasar AFCON 2019 — ta karshe da aka buga gabanin wannan ta 2021 — a yanzu ita ce  zama zakara, Masar ta zo a matsayi na biyu, ita kuma Kamaru mai karbar baki ta z0 na uku.

Kasashen da suka nemi karbar bakuncin AFCON 2021

Bayan taron Majalisar Zartarwa ta Hukumar CAF na a ranar 24 ga watan Janairun 2014, ta sanar cewa kasashen Aljeriya, Guinea da kuma Ivory Coast, na takarar karbar bakuncin gasar AFCON 2021.

Sauran kasashen uku da suka nema kuma aka yi watsi da bukatarsu a lokacin sun hada da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo, Gabon da kuma Zambiya.

Sai dai an samu sabani tsakanin wannan jerin kasashe da suka yi takarar wanda ya bambanta da jerin kasashen da suka nemi karbar bakuncin gasar na shekarun 2019 da kuma 2012 kamar yadda Hukumar CAF ta sanar a Nuwambar 2013.

A kan haka ne aka tsawaita wa’adin kasashen da ke neman karbar bakuncin gasar domin bai wa Hukumar CAF damar tantance duk wata cancanta da kuma sharudan da suka danganci bukatar karbar bakuncin gasar.

A ranar 20 ga watan Satumban 2014, bayan kammala zaben kasashen da suka yi takarar neman karbar bakuncin gasar da aka gudanar a taron Majalisar Zartarwar na Hukumar Kwallon Kafar Afirka, aka mika wa kasar Kamaru karbar bakuncin gasar ta 2019. Ita kuma Ivory Coast aka ba ta masaukin bakin gasar ta shekarar 2021, inda kuma kasar Guinea aka damfara mata gasar 2023.

Dalilin sauya kasashen da za su karbi bakunci

A ranar 30 ga watan Nuwambar 2018 ne Hukumar CAF ta kwace damar karbar bakuncin gasar AFCON 2019 daga hannun kasar Kamaru a sakamakon jinkirin da ta yi na kammala duk wasu gine-gine na filayen wasanni da saurar gine-gine da ake bukata domin kasar ta cika sharudan karbar bakunci.

Hakan ne ya sa aka bai wa kasar Masar damar karbar bakuncin gasar ta 2019, inda Shugaban Hukumar CAF Ahmad Ahmad ya ce Kamaru ta amince za ta karbi bakuncin gasar ta 2021 a madadin damar da subuce mata.

A yanzu ke nan Ivory Coast wadda aka tsara za ta karbi bakuncin gasar AFCON 2021, ita ce za ta karbi bakuncin gasar a 2023, Guinea kuma wadda aka bai wa masaukin bakin gasar AFCON 2023, za ta karbi bakuncin wadda za a gudanar a 2025.

Duk dai wannan shugaban na CAF ne ya tabbatar da hakan ciki wata sanarwa da ya fitar bayan ganawa da Shugaban Ivory Coast, Allasane Outtara, a ranar 30 ga watan Janairun 2019 a birnin Abidjan.

Tarihin Gasar AFCON

Ita dai wannan gasa ta cin Kofin Nahiyyar Afirka da a harshen Ingilishi ake kira da AFCON (Africa Cup of Nations) ko kuma a Faransanci, Coupe d’Afrique des Nations (CAN), an fara ta ne a shekarar 1957.

An kirkiro gasar ce a watan Yunin 1956, wato shekaru 66 ke nan da suka gabata, tun kamin mafi yawan kasashen nahiyar su sami ’yancin kansu daga turawan mulkin mallaka, kuma ana gudanar da ita a duk bayan shekara biyu.

An kirkiro wasan a lokacin taron Hukumar Kwallon kafa ta duniya wato FIFA a  a birnin Lisbon na kasar Portugal.

Gasar AFCON ta farko an gudanar da ita ne a kasar Sudan a yayin kafa Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka a Khartoum, babban birnin kasr, a 1957.

Sai dai a shekarar da aka fara gasar, 1957, kamar yadda tarihi ya nuna, an fara gasar ne da kasashe uku rak, kasancewar mafi yawan kasashen Afirka na karkashin mulkin mallaka, don haka a wancan zamanin, kokarin samun ’yancin kai ake ba ta kwallon kafa ba.

Kasar Afrika ta Kudu wacce na cikin kasashen da aka kirkiri gasar da ita lokacin tana karkashin mulkin ’yan nuna wariyar launin fata da a Turance ake cewa Apartheid, sai aka hana ta shiga gasar bisa dalilin nuna kin jinin bakar fata domin a wancan lokaci kasar ta dage a kan lallai sai fararen fata ne za su wakilce ta, inda ta ki amincewa a sanya bakaken fata a tawagar da za ta wakilci kasar ta su.

Kasashen da suka lashe AFCON da wadanda suka karbi bakunci

1957

A shekarar da aka fara gasar, Kasar Afrika ta kudu ta fice wanda ya ba kasar Masar nasarar lashe kofin gasar bayan Diab Al Attar ya zirara kwallaye 4 a ragar Habasha a wasan karshe wanda Sudan ta karbi bakunci.

1959

Masar ta sake lashe kofin tsakanin kungiyoyi uku da suka shiga gasar inda Sudan ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Masar.

A wannan lokacin Masar da ta karbi bakuncin gasar tana hade ne da Syria a matsayin kasa daya mai suna Hadaddiyar Jamhuriyar Larabawa wato United Arab Republic.

1962

A shekarar 1962, kasar Habasha da ta kasance mai masaukin baki ta samu sa’a a kan Masar da ci 4-2 a wasan karshe.

Hakan ne kuma ya janyo hankalin Tunisiya da Uganda su shiga gasar a karon farko.

1963

Ghana ce ta lashe gasar a karon Farko bayan lallasa Sudan da ci 3-0.

A lokacin an samu karin kasashe zuwa shida da suka shiga gasar, lokacin ne kuma Masar ta lallasa Najeriya da ci 6-3 a gasar da Ghanan ta karbi bakunci.

1965

Kasar Ghana ce ta sake lashe kofin gasar da aka gudanar tsakanin kasashe shida inda ta lallasa Tunisiya mai masaukin baki da ci 3-2.

1968

Kasar Habasha ce ta karbi bakuncin gasar da ta kunshi kasashe 8 da har ya kai aka buga wasan kusa da karshe.

A lokacin kasar Jamhuriyyar Kongo ce ta lashe kofin bayan ta doke Ghana da ci 1-0.

1970

Kazalika, Ghana ta buga wasan karshe tsakaninta da Sudan, amma Sudan mai masaukin baki ta lashe kofin gasar da ci 1-0.

1972

A shekarar ce kasar Kongo Brazzaville ta lashe kofin bayan ta samu sa’ar kasar Mali da ci 3-2 a birnin Yaounde na kasar Kamaru.

1974
A karon farko a shekarar 1974 ne aka maimaita wasan karshe tsakanin Kongo da Zambiya, amma kasar Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo ce ta lashe kofin da ci 2-0 bayan sake fafatawa a birnin Alkahira na kasar Masar da ta karbi bakunci.

1976

Kasar Mor0ko ce ta lashe gasar bayan samun rinjayen maki fiye da kasar Guinea a gasar da aka gudanar a kasar Habasha.

1978

Ghana ta lashe kofinta na uku a gasar da aka buga a kasarta bayan Opoku Afriyie ya zira kwallaye biyu a ragar Uganda a birnin Accra.

A wannan lokacin Najeriya ta samu matsayi na uku bayan Tunisiya ta fice a karawar neman na uku.

1980

Najeriya da ta karbi bakunci ta samu sa’a karon farko na lashe kofin gasar a gida bayan lallasa Aljeria 3-0.

1982

A 1982 Ghana ta lashe kofinta na hudu bayan ta doke Libya mai masaukin baki da ci 7-6 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A shekarar ce kuma Abedi Pele ya fara haskawa kafin ya zama fitaccen dan wasa a duniya.

1984

Kasar Kamaru ce ta lashe kofin gasar bayan ta doke Najeriya da ci 3-1 a gasar da aka buga a kasar Ivory Coast.

1986

Masar ta sake lashe kofin gasar a bugun fenariti tsakaninta da Kamaru a birnin Alkahira na kasar Masar.

1988

Karo na uku da kasar Kamaru ke zuwa zagayen karshe a jere, inda ta sake lashe kofin bayan ta doke Najeriya a gasar da aka buga a Moroko.

1990

A shekarar ce Aljeria mai masaukin baki ta lashe kofin bayan ta doke Najeriya a wasan farko da wasan karshe.

1992

A wannan karon ne gasar ta koma tsakanin kasashe 12, kuma a shekarar ce aka buga wasan karshe tsakanin Cote d’Ivoire da Ghana a Senegal. Kasar Cote d’Ivoire ce ta lashe kofin gasar ci 11-10 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

1994

Najeriya ce ta lashe kofin gasar da aka buga a kasar Tunisiya bayan doke Zambiya da ci 2-1 bayan hadarin jirgi ya kashe ’yan wasan Zambiya a kasar Gabon.

1996

A shekarar ce aka fara gudanar da gasar tsakanin kasashe 16 inda kasar Afrika ta Kudu ta fara haskawa bayan kwashe shekaru ana gudanar da gasar ba tare da ita ba saboda rikicin cikin gida.

Afrika ta Kudu da ta karbi masaukin baki ce dai ta lashe kofin gasar bayan doke Tunisia da ci 2-0.

1998

Kasar Afrika ta Kudu ta sake samun kaiwa zagayen karshe, amma Masar ce ta lashe kofin gasar da aka gudanar a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso.

2000

A Najeriya aka gudanar da gasar kuma kasar Kamaru ce ta samu nasarar lashe kofi bayan doke Najeriya da ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

2002

Kasar Kamaru ce ta lashe kofin gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida tsakaninta da Senegal a Bamako.

2004

Kasar Tunisiya da ta karbi bakunci ce ta lashe kofin gasar bayan doke Moroko da ci 2-1.

2006

Masar mai masaukin baki ta lashe kofin a wasan karshe tsakaninta da Code d’Ivoire.

2008

Masar ta kare kambunta bayan samun nasara a wasan karshe tsakaninta da Kamaru wanda aka buga a Ghana.

2010

A shekarar ce Masar ta lashe kofin gasar sau uku a jere a birnin Luanda na kasar Angola bayan doke kasar Ghana.

2012

Zambiya ce ta lashe kofin gasar a birnin Libreville bayan doke Cote d’Ivoire ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A lokacin manyan kasashe da suka yi fice a gasar ba su samu damar tsallakewa ba da suka hada da Masar da Kamaru da Najeriya da Aljeriya.

A Shekarar ce kasar Nijar ta fara haskawa a gasar karon farko wadda Gabon da Equatorial Guinea suka kasance masu masaukin baki.

2013

An janyo gasar AFCON 2014 zuwa AFCON 2013 domin gudun kada gasar ta rika cudanya da lokacin da ake buga gasar Kofin Duniya da galibi take zuwa a shekarun mara.

Gasar wadda aka tunkuda ta zuwa shekaru masu wutiri, Afirka ta Kudu ce ta yi mata masaukin baki, kuma Najeriya ta lashe bayan Sunday Mba ya zura kwallo daya tilo a ragar Burkina Faso a wasan da aka fafata a Johannesburg, Afirka ta Kudu.

2015

Equatorial Guinea ce ta yi wa gasar AFCON 2015 masaukin baki, kuma Ivory Coast ta samu nasara a kan Ghana a wasan karshe wanda ta kai ga sai da duk ’yan wasa 11 na kowane bangare suka yi bugun fenaretin da aka karkare 9-8.

2017

A Gabon aka buga gasar AFCON 2017, wadda a karo na biyar ke nan kasar Kamaru ta lashe bayan lallasa Masar da ci 2-1 a wasan karshe.

2019

An buga gasar AFCON 2019 a tsakanin 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga Yulin 2019, tsukin shekara guda ke nan bayan ta 2018 da aka buga.

A ranar 20 ga watan Yulin 2017 ce Hukumar Kwallon Kafar Afirka CAF ta sauya lokacin gasar da ake bugawa a tsakanin watan Janairu da Fabrairu zuwa watan Yuni da Yuli.

Wannan gasar da aka fafata a kasar Masar ita ce irinta ta farko da aka fadada a tsakanin tawagar kasashe 24 sabanin 16 da ake yi a baya. Aljeriya ce ta lashe gasar bayan ta yi wa Senegal ci daya mai ban haushi.

2021

Kamaru ce ta yi wa AFCON 2021 masaukin baki kuma Senegal ta samu nasara bayan ta doke Masar a bugun daga kai sai mai tsaron raga.