Ranar Laraba 6 ga watan Mayun 2020 ne adadin wadanda suka kamu da coronavirus a fadin duniya ya haura miliyan 3.6, yayin da miliyan 1.2 suka warke daga cutar inda ta hallaka fiye da mutum 252,000.
A Najeriya an samu mutum na farko dauke da cutar a ranar 27 ga watan Fabrairu kuma zuwa daren 6 ga watan Mayu akwai adadin masu fama da cutar 2,950 yayin da aka sallami 481, mutum 98 kuma suka riga mu gidan gaskiya.
Cutar sarkewar numfashin da ta fara bulla a karshen shekarar 2019 a birnin Wuhan na kasar China yanzu ta yadu zuwa fiye da kasashe 180 na duniya.
Kasashen da basu samu mai cutar coronavirus ba
Wadannan su ne kasashen da har yanzu ba a samu mai dauke da cutar coronavirus a cikinsu ba har zuwa ranar 30 ga watan jiya:
- Kiribati
- Lesotho
- Marshall Islands
- Micronesia
- Nauru
- Koriya ta Arewa
- Palau
- Samoa
- Solomon Islands
- Tonga
- Turkmenistan
- Tuvalu
- Vanuatu
Kasashen da ba ta kashe kowa ba
Akwai kuma kasashen da ba a samu mutuwar ko mutum guda sakamakon cutar ba, kamar yadda alkaluman wata kafar intanet mai suna Worldometer suka nuna – a wadannan kasashen an samu waraka 100 bisa 100 na mutanen da suka kamu da coronavirus:
Falkland Islands
Tsibirin Falkland ya shaida kamuwar mutum 13, sai dai dukkansu sun murmure daga cutar.
Sai kuma tsibirin Greenland
Tsibirin Greenland ita ma ta samu masu cutar su 11 kuma duk sun warke, tsaf. Tsibirin Greenland dai shi ne mafi girma a duniya – yana tsakanin tekun Arctic da Atlantic, gabas da yankin Arctic Archipelago na Canada.
An shafe makonni ba tare da an sami sabon wanda ya kamu da cutar a Greenland. A ranar 4 ga watan Mayu, an dage dokar hana fita daga kasar, kamar yadda gwamnatin ta sanar a shafinta na yawon bude ido.
Papua New Guinea
Papua New Guinea, PNG, wacce take da masu cutar su takwas kuma duk sun warke. Kasar tana kudu maso yammacin Pacific.
A ranar 20 ga watan Maris, aka gano mutum na farko mai dauke da cutar coronavirus a kasar – wani ma’aikacin hakar ma’adinai dan kasar waje – kuma kwana biyu bayan nan kasar ta sanar da saka dokar ta baci, inda aka takaita zirga-zirga da kuma taron jama’a da ma wasu matakan, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Saint Barthélemy
Kasar Saint Barthélemy ta samu masu cutar guda shida wanda dukkansu suka warke. Kasar wacce take a tsibirin Carribean kuma take amfani da harshen Faransanshi an fi saninta da suna St. Barts,
Gwamnatin kasar ta tabbatar da samun mutum biyu a karon farko masu dauke da cutar a tsibirin a ranar Lahadi 15 ga watan Maris. An killace duk mutanen biyu a gidajensu.
Anguilla
Tsibirin Anguilla ta samu mutum uku dauke da cutar wadanda suka warke daga bisani.
Anguilla, wani tsibiri ne da ke karkashin ikon Birtaniya a Gabashin yankin Caribbean.
Yana nahiyar Arewacin Amurka. A cikin watan Afrilu kasar ta sanar da dage matakan takaita zirga-zirgar jama’a da taruka, bayan shelar da aka yi cewa ‘babu wani da ya rage dauke da cutar ko wanda ake zargin yana dauke da ita a tsibirin.
Dage haramcin ya biyo bayan da Babban Jami’in Kiwon Lafiya na tsibirin ya fadawa Majalisar Zartarwar Anguilla cewa, za a iya dage haramcin ba tare da ya haifar da wata matsala ba – kamar yadda wata kafar labarai a yankin ta sanar.