Kungiyar da ke kan gaba wajen shirya zanga-zangar #EndSARS a Najeriya ta bukaci masu zanga-zangar da su hakura su zauna a gida.
Kungiyar Feminist Coalition ta shafukanta na sada zumunta, ta yi fatar a kawo karshen tattakin da matasa shafe sati biyu suna yi a fadin kasar, wadda daga bisani ta koma tarzoma musanman a Jihar Legas da wasu jihohin kasar.
- #EndSARS: Buhari na ganawa da tsoffin shugabannin kasa
- Muhimman abubuwa 12 daga jawabin Buhari kan zanga-zangar #EndSARS
- A dakatar da Zanga-zangar #EndSARS —Shugabannin Kudu
A sanarwar kungiyar ta ce ba za ta sake karbar wata gudummawar kudi da sunan #EndSARS ba, sannan ta bukaci matasan da su bi dokar hana fita da aka saka a wasu jihohi.
Ta bayyana cewa ta tara kimanin Dalar Amurka 400,000 na gudummawa daga sassan duniya, kuma har yanzu ba a kashe kudaden ba.
Kungiyar ta fitar da sanarwar ne bayan sa’o’i da jawabin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis.
Buhari, a jawabinsa, ya bukaci matasa su dakatar da zanga-zangar ta #EndSARS, saboda ci gaba da gudanar da ita “zai jawo wa tsaron kasa matsala kuma ba zai lamunci hakan ba”.