A ranar Talata da ta gabata ce fitaccen dan wasan kwallon kafar nan, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin zura kwallo uku rigis a raga.
Ya kafa tarihin ne bayan ya zura kwallayen a ragar Luxembourg, yayin wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya.
- Yadda mahari ya hallaka mutum 5 da kwari da baka a Norway
- An kama Dodanni kan zargin fashi da makami a Ondo
Ronaldo ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida ne, sannan ya jefa ta uku a raga da kai.
Wadannan kwallayen da ya zura, shi ne karo na 58 da ya ci kwallo uku rigis a wasa guda a kwallon kafa.
Da wannan, kyaftin din na Portugal ya zama na farko da ya zura kwallo uku rigis har sau 10 a kwallon gida.
Yanzu Ronaldo na da kwallo 115 a kwallon gida.
Haka kuma, ya kara gaba a jerin wadanda suka fi zura kwallo a kwallon gida, inda yanzu yake gaba da na biyu a jerin, wato tsohon dan wasan kasar Iran, Ali Daei, wanda ya rike kambun na tsawon shekara 15 kafin Ronaldo ya kwace shi.
A cikin ’yan kwallon da ke cigaba da kwallo a yanzu, Lionel Messi ne ke biye masa, inda yake a na biyar da kwallo 80.
Wannan ya sa Aminiya ta rairayo kasashe guda 10 da Ronaldo ya zuba wa kwallo uku a raga.
Northern Ireland: 2013: Wasan neman shiga Kofin Duniya na 2014
Sweden: 2013: Wasan fidda gwani na Kofin Duniya na 2014
Armenia: Wasan neman shiga gasar EURO ta 2016
Andora: 2016: Wasan neman shiga Kofin Duniya na 2018
Tsibirin Faroe: 2017: Wasan neman shiga Kofin Duniya na 2018
Spain: 2018: Gasar Kofin Duniya ta 2018
Switzerland: 2019: Gasar UEFA Nations League
Lituania: 2019: Wasan shiga Kofin Nahiyar Afirka na 2020
Lituania: 2019: Wasan shiga Kofin Nahiyar Afirka na 2020
Luxembourg: 2021: Wasan shiga Kofin Duniya