kasar Sin watau Chaina ta ce tuni ta fara zawarcin dan kwallon Ingila da kulob din Manchester United Wayne Rooney don ganin ya koma can don ya cigaba da yin kwallo.
Kamar yadda jaridar The Sun ta Ingila ta ruwaito, Sin tana zawarcin dan kwallon ne don ya taimaka wajen bunkasa harkokin kwallo a kasar.
Kodayake dan kwallon yana da sauran shekaru uku kafin ya gama kwantaraginsa a kulob din United akwai yiwuwar kasar ta dauke shi muddin ya amince da tayin da ta yi masa na biyan sa makudan kudi a matsayin albashi da kuma alawus-alawus.
Rahoton ya ce Sin ta fara yunkurin farfado da gasar rukuni-rukunin kasar ne bayan ta samu tallafi daga manyan gidajen talabijin na kasar wadanda suka kuduri aniyar zuba jari mai kauri a harkar kwallon kafa.
Rahoton ya ce Rooney yana daya daga cikin ’yan kwallon da kasar ke ganin za su bunkasa harkokin kwallonta, don haka take yunkurin ganin ta dauke shi ko ta halin kaka. Kawo yanzu Rooney ya zura kwallaye 7 daga cikin wasanni 18 da ya yi a bana.
kasar Sin ta fara zawarcin Rooney
kasar Sin watau Chaina ta ce tuni ta fara zawarcin dan kwallon Ingila da kulob din Manchester United Wayne Rooney don ganin ya koma can…