Kasar China ta haramtawa daliban makarantun Firamare da na Sakandire amfani da wayoyin salula a kokarin da take yi na takaita yawan shiga yanar gizo da kuma wasanni da na’ura mai kwakwalwa.
A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimin Kasar, daga yanzu dole dalibai su kaucewa zuwa azuzuwa da wayoyin nasu.
- An daure shi a gidan yari saboda zagin tutar China
- Fadar Shugaban Kasa ta yi barazanar sake dawo da dokar kulle
Kazalika, sanarwar ta ce ga dukkan dalibin da yake son amfani da wayar a makaranta, dole ya kawo rubutaccen izini daga iyayensa.
Ma’aikatar ta ce da zarar sabuwar dokar ta fara aiki, dole kowanne dalibi ya damka wayar ga hukumar makarantarsa da zarar ya shigo sannan ba za a bar daliban su shiga aji da su ba bisa kowanne irin dalili.
Kasar ta kuma ce za ta samar da hanyoyin da yaran za su iya tuntubar iyayensu daga makarantun idan bukatar hakan ta taso.