✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin kudin badi zai haura naira tiriliyan 7

Fadar Shugaban kasar ta ce aiki ya yi nisa wajen shirya gagarumin kasafin kudin shekarar 2016, wanda ake gani zai haura naira tiriliyan bakwai.Mataimakin Shugaban…

Fadar Shugaban kasar ta ce aiki ya yi nisa wajen shirya gagarumin kasafin kudin shekarar 2016, wanda ake gani zai haura naira tiriliyan bakwai.
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi tsokacin a wajen taron bitar da aka shirya wa sabbin ministocin kasar  nan 36.
Kasafin kudin kasar da aka shirya na bana, ya kai naira tiriliyan hudu  da doriya. Gwamnatin dai ta shirya aiwatar da gagarumin kasafin ne a daidai lokacin da kasar ke fama da rashin kudi.
Kamar yadda Kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana wa BBC ya ce gwamnatin tana so ta ware fiye da kashi 40 cikin 100 domin gudanar da ayyukan raya kasa, sabanin a baya yadda akwa ware kimanin kashi 70 cikin 100 ga ayyuka yau da kullun.
Ya ce gwamnati za ta nemo kudin ne ta hanyar karbar haraji yadda ya kamata, da kuma wani asusu na hadin gwiwa da bangarori masu zaman kansu.