Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da Naira tiriliyan 13.08 a matsayin daftarin kasafin kudin shekarar 2021, a yayin zaman Majalisar Zartarwa da ya jagoranta a ranar Laraba.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin ganawarta da manema labarai bayan zaman Majalisar Zartarwar da aka yi a fadar shugaban kasa ta Villa da ke Abuja.
- Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 4 a fadarsa
- Buhari ya mika wa sanatoci kasafin 2021 zuwa 2023
Ministar ta bayyana hakan ne yayin da suke tare da Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai Muhammed da Minista a Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare Clement Agba da kuma Darakta Janar na ofishin kasafin kudi na Tarayya, Ben Akabueze.
Ministar ta ce, an kiyasta kudaden da za a kashe kan kadarorin gwamnati da suka kai Naira tiriliyan N2.083, yayin da aka kayyade farashin danyan man fetur kan dalar Amurka $40 duk ganga.
Kasafin kudin 2021 sun hada da: Tace ganga mai miliyan 1.86 a kullum, yayin da za a cire ganga dubu 400 daga cikin danyan man bayan fitar da man fetur.
Ana sa ran za a ware kashi 3 cikin 100 daga kayan da ake samarwa na cikin gida (GDP).
An kuma kiyasta hauhauwa na farashin kayayyaki zai kai kashi 11.95 cikin 100, sannan kuma musayar kudaden kasashe waje kan kowace dalar Amurka daya a kan Naira 379.
Ministar kudin ta ce sabon daftarin kasafin kudin zai samar da ci gaba da samar da aiyukan a kasar.