✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karyar tela

Wani tela ne surikinsa ya ba shi dinki sai ya sanya masa ranar da zai zo ya karba. Da ranar ta zagayo, ya zo karbar…

Wani tela ne surikinsa ya ba shi dinki sai ya sanya masa ranar da zai zo ya karba. Da ranar ta zagayo, ya zo karbar dinki sai tela ya ce: “Baba ka yi hakuri, ban dinka ba amma ka dawo gobe ka karba.” Wanshekare tela yana zaune a kofar shagonsa yana hira sai ya hango surikinsa yana zuwa, sai ya ruga ya shiga shagon, ya ce wa abokan aikinsa cewa su yi sauri su rufe shi da kyallayen yadi, ya kuma ce idan surikin nasa ya zo, su fada masa cewa ya yi tafiya. Ashe wajen rufe shi sun mance ba su rufe kafafunsa ba. Da surikin ya karaso shagon sai telolin suka

isar da sako kamar yadda tela ya bari. Sai surikin ya yi kamar ya yarda, ashe ya ga kafafun telan a waje, sai ya ce wa telolin: “Ku shaida masa cewa nan gaba idan zai yi tafiya, ya yi da kafafuwansa.”
Daga Nura Suleja Neja, 08078983237