Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya faɗo daga matsayinsa na mai arzikin da yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirka sanadiyyar karyewar darajar Naira.
Alhaji Aliko Ɗangote ya riƙe wannan kambin tsawon shekaru 12 amma yanzu ya koma na biyu, a cewar mujallar Forbes mai ƙididdige kuɗin masu arzikin duniya.
Ɗan kasuwar Afirka ta Kudu, Johannes Rupert shi ne ya maye gurbinsa a matsayin maikuɗin Afirka.
Karya darajar Naira: Ba za mu janye labarinmu ba —Daily Trust ga CBN
Muhimman abubuwa kan Matatar Man Dangote
Rahoton da Forbes ta fitar a a ranar Lahadi yace Alhaji Aliko Ɗangote ya yi asarar fiye da $3.4 biliyan a rana guda sakamakon karyewar darajar Naira.
Sauran manyan masu kuɗin Najeriya su ma sun girgiza sakamakon karyewar Nairar.
Alhaji Abdulsamad Rabi’u, shugaban kamfanin BUA ya yi asarar $2.7 biliyan inda ya sauka daga matsayi na huɗu zuwa na shida a jerin masu kuɗin Afirka.
Babban Bankin Najeriya ne dai ya cire wa bankuna takunkumin cinikin Dalar Amurka, abin da ya haddasa faɗuwar darajar Naira.
Wannan ta sa a hukumance canjin ya kai N655/$1 saɓanin N471/$1 a farkon makon da ya gabata.