✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwanci: Labarin Yaganar Maiduguri (2)

  Ci gaba: Mamaki ya ishe ta, ta yi mini wani irin kallo, sannan ta yi dariya, “Me ya sa ka ce haka, kai ma…

 

Ci gaba:

Mamaki ya ishe ta, ta yi mini wani irin kallo, sannan ta yi dariya, “Me ya sa ka ce haka, kai ma dan hannu ne?” Na kara fuskantarta, sannan na yi gajeren murmushi, daga bisani na mayar da hankalina kan tukin da nake yi. Bayan kamar sakan 30 ne sai na kara fuskantarta, sannan na fara magana, “kina gani kamar ni ma na san dawar garin ne? Ko na yi kama da dan hannu?” Ta yi mini wani irin kallo. “Yaya ina tambayarka, maimakon ka ba ni amsa sai ka kuma sake tambayata?” Ta tsayar da kallonta gare ni. Na sake yin murmushi.
“Amma idan aka ce ki fadi abu a kaina bisa ga yanayina me za ki ce?” Na tambaye ta ba tare da na kalleta ba, kasancewar ina kokarin yin kiliya da wata motar dangote da ta dauko buhun siminti, inda a bayanta kuma, wadansu kananan motocin bas-bas ke biye da ita alamar ransu a bace yake domin ta hana su wucewa.
“Ka yi kama da wayayyun mutane, wadanda suka san duniya, suka kuma iya mu’amala da mutane.” Ta ce da ni a lokacin da take ci gaba da danne-dannen wayarta. Na yi dariya, dariyar da ta sanya ta yi saurin fuskantata. “Amma kin burge ni….” Zaro idanun da ta yi ne ya tsayar da ni, sannan na bi ta da kallo, daga bisani na ce mata, “Za ki tsorata ni, irin wannan zare ido sai ka ce na yi gamo da soja?” Ta yi wata munafukar dariya, sannan ta fara magana, “Malam, ka cika ban dariya fa, na gane ka, lauye-lauye kake ta yi don kada ka fada mini ko kai dan hannu ne ko a’a.”
Muna cikin haka ne sai muka iso wani kauye da ake kira Zaranda, na yi fakin a kusa da wani masallaci, sannan na fuskance ta, hakan ne ya sanya ta tattara hankalinta gare ni, bayan ta rike wayarta a hannunta na dama wanda yake dauke da kunshi mai daukar hankali. Ganin ta ci gaba da kallona ne, na ce mata, ina son shan wani abu ne, don haka mai zan saya mata. Daga farko ta nuna ba ta son komai, amma na takura mata, a nan ta ce in saya mata Maltina. Na sayo lemon Coke, ita kuma na saya mata Maltina da biskit din Short Bread, sannan na sayi kankana da ayaba da kuma abarba, sannan na sanya aka yanyanka su.
Na dawo cikin mota na same ta tana amsa waya, haka na bude kofar motar na shiga, inda ta kalle ni, sannan ta ci gaba da wayarta. Bayan na ajiye ledojin da ke hannuna a kujerar bayan motar ne na tashi motar, na yi addu’a, sannan na nausa kan hanya, ban dade da fara tafiya ba, ta gama wayar da take yi. Kana jin wayar ka san da namiji dan hannu take yi, kasancewar akwai miskilanci a tattare da kalamanta. A nan na bukaci ta mika hannunta ta dauki ledar da ke dauke da Maltina da kuma lemon Coke da biskit. Ba ta ce komai ba ta dauko, na ce mata ta miko mini Coke, ta sha Maltinar. Abin da ya ba ni mamaki, ba miko mini Coke din kawai ta yi ba, face sai da ta bude mini. Na karba, na yi mata godiyar bude mini da ta yi, sannan na fara sha.
Ina ganin lokacin da ta bude Maltinarta ta fara sha, a lokaci guda ta ci gaba da cin biskit dinta. Bayan ta dauki lokaci tana ci ne, sai ta tambaye ni ko ba zan ci biskit din ba ne? Gudun magana, sai na dauka na fara ci, ina ganin lokacin da ta saci kallona, na yi dariya a cikin zuciyata domin na san wani abu zai biyo baya. “Malam kai miskili ne, ka kwashe ni da hira, ko sunanka ban sani ba. Na rasa ma yadda aka yi na biye ka muke ta surutu, ni ban saba haka ba.” Ta ce da ni bayan ta ajiye cire kwalbar Maltinar daga bakinta. Na gane nufinta, hakan ya nuna tana jin dadin hira da ni. Na kara yin murmushi domin na gaskata kaina. Bayan na dauke kallona daga kan titi, sai na ce mata, “Sunana Bashir, ni dan karamar Hukumar Jama’are da ke Jihar Bauchi ne, amma aiki ya kai ni Jos, yanzu da kika gan ni na dawo daga hutun karshen mako ne.” Na yi shiru, sannan na ci gaba da tuki, bayan wadansu dakiku, sai na ce “Ba ki tambaye ni aikin me nake yi ba?”
“Saurin magana ka yi amma ina shirin in tambaye ka ke nan.” Na yi dariya, sai na ce mata “Aikin yankan kai nake yi….” Na yi shiru ina kallonta, ta yi dariya, daga bisani ta ce, “Wallahi kai miskilini, ka sani ai me yi ba ya fada, tuni zuciyata ta gamsu, kai mutumin kirki ne, kuma kai tsaye na ji zuciyata ta gamsu ba za ka cutar da ni ba.” Na yi dariyar jin dadi a cikin zuciyata, domin shigo-shigon ba zurfin da nake yi mata ya fara kama ta, ina so ta sake da ni don in yi mata dukkan tambayoyin da nake so ba tare da ta yi zargin wani abu ba.
Don jin yadda za ta kasance, sai mako na gaba idan Allah Ya kaimu.