Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta ceto wasu ’yan mata uku da ake kokarin jefa su sana’ar karuwanci a unguwar Itamaga da ke Ikorodu ta jihar.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
- Kotu ta tsare matashin da ya kashe kanwarsa da matar babansa
- Yadda mata ’yan NYSC ke fama da tsadar haya a Abuja
Hundeyin ya ce an kubutar da ‘yan matan ne a ranar 8 ga watan Janairu da misalin karfe 6:00 na Yamma, a lokacin da tawagar ‘yan sandan sintiri suka lura ana kokarin safararsu a yankin.
“Da aka tambaye su, ‘yan matan sun bayyana cewa sun gudu ne daga hannun wata uwar gidansu da ta kawo su daga Akwa Ibom zuwa Legas da sunan neman aiki,” in ji shi.
Ya ce binciken ya nuna cewa uwar gidan tasu ta kulle su sannan ta hana su abinci.
“Da isar ‘yan matan Legas, uwar gidansu ta kulle su a wani otal, inda suka sha fama da yunwa ta tsawon kwanaki domin tilasta musu shiga karuwanci.
“An tuntubi iyayen wadanda abin ya shafa,” in ji shi.
Ya ce Kwamandan RRS, CSP Olayinka Egbeyemi, ya mika wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa sashen kula da safarar mutane na Jihar Legas domin ci gaba da bincike.