✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

KAROTA za ta tara Naira biliyan 1 a 2021

Hukumar Sufuri ta Jihar (KAROTA) ta bayyana kudurinta na tara harajin Naira biliyan daya a shekarar 2021. Shugaban KAROTA, Bappa Babba Danagundi ne ya bayyana…

Hukumar Sufuri ta Jihar (KAROTA) ta bayyana kudurinta na tara harajin Naira biliyan daya a shekarar 2021.

Shugaban KAROTA, Bappa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan yayin da yake kare kasafin hukumar a gaban Majalisar Dokokin jihar a ranar Litinin.

Danagundi ya ce, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya amince wa hukumar ta dauki sabbin ma’aikata 1,400.

Ya ce a yanzu haka sun samu nasarar daukar sabbin ma’aikata 700, kuma nan da watan Janairun sabuwar shekara za su dauki ragowar 700.

%d bloggers like this: