Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) za ta dauki sabbin ma’aikata 700, dominkara wa jami’ai 2,500 da take da su a Jihar karfi.
Manajan Daraktan Hukumar, Baffa Dan’agundi, ya za a tura sabbin jami’an ne su yi aiki a sabbin masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano domin tabbatar da kiyaye dokokin ababen hawa.
- ‘Ciyar da daliban Kano kan lakume N4bn duk shekara’
- Gwamnan Jigawa ya gabatar da kasafin 2021
- Yadda Najeriya za ta bunkasa kasuwanci da fasahar zamani — NITDA
Dan’agundi ya kuma gargadi ‘yan talla da ke neman dawowa kan tituna da sauran wuraren da aka haramta yin hakan a birnijn Kano.
“Mun tsananta domin ganin ‘yan tallan da aka tayar ba sake dawowa suna haddasa wa masu amfani da tituna matsala ba”, inji shi.
A cewarsa, nan gaba hukumarsa za ta yi hadin gwiwa da Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar Kano (KARMA) domin gyaran tituna da ke cikin birnin Kano da kewaye.