Gwamnatin Jihar Kano ta haramta yin goyo a kan babura masu kafa biyu saboda zargin dawowar sana’ar acaba a jihar.
Hukumar Kula da Harkokin Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA)
ta ce matakin ya zama wajibi kuma za ta fara kama masu karya dokar daga ranar Alhamis 18 ga watan Yuni.
“Mun lura wasu na son dawo da sana’ar acaba, don haka muke gargadin jama’a cewa dokar haramta goyo tana nan daram kuma za mu fara aiki a kanta daga ranar Alhamis.
“Idan aka bude gari muka kama mutum ya yi goyo a babur mai kafa biyu to ba za mu saurara masa ba”, inji shi.
Tun a shekarun baya da hare-haren kungiyar Boko Haram suka yi kamari Gwamnatin Jihar Kano ta fara haramta yin goyo a babura masu kafa biyu gaba daya sakamakon yawaitar zargin maharan kungiyar da amfani da su.
Dan’agundi ya kuma yi kira ga jama’a musamman masu ababen hawa da su rika yin amfani da takunkumin rufe hanci a duk lokacin da suke kan titi don gujewa kamuwa da cutar coronavirus.