✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karon ’yan sanda da masu fafutikar ceton ’yan mata

’Yan sanda sun yi wani sauyin tunani mai kyau a Alhamis din makon jiya, inda suka kyale aka gudanar da zanga-zangar neman ceto ’yan matan…

’Yan sanda sun yi wani sauyin tunani mai kyau a Alhamis din makon jiya, inda suka kyale aka gudanar da zanga-zangar neman ceto ’yan matan Chibok, a karkashin kungiyar #BringbackOurGirls, har ma tsaro da rakiya suka yi musu zuwa fadar Shugaban kasa, don isar da sakon nuna takaicinsu ga Shugaban kasa. Hukumomin ’yan sanda a Babban Birnin Tarayya sun taba yin barazanar dakatar da taron matan dake zanga-zanga, wadanda suka zargi gwamnati da kasa yin katabus wajen ceton ’yan matan Chibok, su 276, ’yan makaranta da suka fito daga Jihar Barno, wadanda ’yan Boko Haram suka sace a ranar 14 ga Afrilu.
Wannan mataki da ’yan sanda suka dauka, ya yi daidai da abin da jami’an sun sha kwata irin wannan tun farko a karon su da masu fafutika a Abuja da Kaduna da Lokoja. Duk da cewa masu fafutika sun taru ne don yi zanga-zangar luma a wurin shakatawa na ‘Unity Park’ da ke Abuja, sai aka ga taron ’yan sanda dauke da makamai sun iso, sun tare wurin, sun hana ayi taron, suka tarwatsa wadanda suka shirya gangamin. A cewar ’yan sandan, sun samu “umarni daga sama’ kan su dauki matakin hana ci aba da zanga-zangar neman ceton ’yan matan Chibok. Irin wannan angamin da aka gudanar a Kaduna, ’yan sanda sun dakatar da shi, ta hanyar amfani da jami’an hana tarzoma da motar yaki da suka girke a dandalin Murtala Mohammed, don tabbatar da cewa sun hana a gudanar da duk wani gangami. A Lokoja ma, ’yan sanda sun sanar da wadanda suka shirya gangamin a rubuce, inda suka yi musu nuni da kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar, don haka suka ki amince da duk wani taron jama’a.
Yadda ’yan sanda suka tarairayi al’amari, wannan na nuni da rashin sanin makamar aiki kan yadda za su kula da masu zanga-zangar lumana, kan lamarin da ya zama abin tsokaci a daukacin fadin duniya. Irin wannan rudanin gwamnati ce ta haifar da shi don karya lagon wadanda ke yi mata matsin lamba kan lallai ta kara kokari fiye da abin da take yi, wajen ceto ’yan matan Chibok da aka sace.
Dole ’yan sanda su fahimci hakkin mutane na gudanar da zanga-zangar lumana, sannan sub a su tsaro a duk sa’adda bukata ta taso. Masu fafutikar, tamkar iyaye ne su kansu, wadanda suka nuna damuwarsu, bisa la’akari a tande-tanaden dokokoki, wajen shirya gangami don jawo hankulan al’umma game da mummunan abin da ya auku a kan ’yan matan Chibok.
Wannan yunkuri da aka yi ya sanya kusan ko’ina cikin manyan biranen duniya, an yi irin wannan gangamin.. wannan ba a bin mamaki ba ne irin matakin da suka dauka, ta hanyar hadin gwiwa da kungiyoyin fafutikar hakin al’umma da kafafen yada labarai, har ta kai ga an fara fafutika a daukacin fadin duniya, ta hanyar da gudunmuwar sojoji daga gwamnatocin kasashe, wadanda za su taimaka wa gwamnati ta ceto ’yan matan, ta kuma samu shawo kan matsalar Boko Haram. Don haka babu wata alamar tambaya a kan wannan gangami, ballantana a ce zai kawo wa ’yan sanda wani cikas. Don haka sauya tunanin da ’yan sandan babban birnin tarayya suka yi, mataki ne mai kyau, kuma abin koyi ga daukacin fadin kasar nan.
Daga cikin darussa da dama da aka fahimta kan matakin da ’yan sanda suka dauka, dangane da gangamin al’umma kan fafutikar ceto ’yan matan Chibok ta “#BringbackOurGirls”, shi ne yadda jami’an tsaro ke bai wa kansu karfin ikon yanke hukunci, a lokacin da mutane ke ke yin gangami don nuna damuwarsu kana bin da ya shafi al’umma. Ya kamata gwamnati ta daina mayar da hankali kan takaddamar da ake yi a wajen zanga-zanga, abu mafi a’ala’ shi ne a dukufa wajen gano musababin faruwar al’amarin.
An kafa hujja bisa dogaro da tanade-tanaden doka, kan cewa al’umma na da hakkin shirya gangami, kamar yadda yake kunshe a sashi na 40 na Kundin tsarin mulkin Najeriya, da Dokar Afirka kan ’Yancin dan Adam, wadda bai kamata a saba mata ba, domin Najeriya na cikin jerin kasashen da suka rattaba mata  hannu. Wannan hujjar ta samu tsayuwa da karfinta bisa la’akari da hukunce-hukuncen manyan kotuna suka yanke, wadanda suka hada da Kotun koli ta Najeriya.
’Yan sanda na yawan karya dokar kula da al’umma (Cap 382) da ke cikin dokokin Tarayyar Najeriya wajen amincewa ko akasin haka game da bukatar shirya taron jama’a, duk a cewa kotuna sun yanke hukuncin cewa tanadin doka daidai yake da abin da ke kunshe a kundin tsarin mulki. Wannan shi ne sakon da sakon da ya kamata hukumomin ’yan sanda su rika aiki da shi, bayan da suka sha turkaniya kan ’yan matan Chibok da aka sace, a daidai lokacin da zabe ke karatowa.