✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karon battar tsofaffin gwamnonin da ke neman shugabancin APC

Yawaitar ’yan Arewa masu neman shugabancin kan iya zama tarko ga Kudu.

Ana ci gaba da fafata neman kujerar Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, inda manyan ’yan siyasa suka fara bayyana kansu.

Hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta fara gudanar da taron zaben shugabanninta tun daga matakan unguwanni zuwa kananan hukumomi, zuwa jihohi da shiyyoyi, inda a karshe za a gudanar da babban taronta na kasa don zabar mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC).

Kuma a wani bangare na hakan shugabannin jam’iyyar, sun samu a matakan unguwanni da kananan hukumomi, sakamakon zabensu da aka yi a watan Agusta da Satumba.

Kuma ganin ba a kammala da batun rarraba mukamai zuwa shiyya shiyya ba, masu neman tsayawa takarar mukamai daban-daban a gama ba tukuna, masu neman mukamai daban-daban suna ta aiki ta karkashin kasa gabanin babban taron jam’iyyar.

A halin yanzu Jam’iyyar APC tana karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, wanda ya karbi jagorancinta a ranar 25 ga Yunin 2020, bayan rushe Kwamitin Gudanarwa da Adams Oshiomhole yake jagoranta.

Ana sa ran kwamitinsa ya shirya babban taron jam’iyyar kafin karshen bana.

Ana ci gaba da tataburzar ganin an mika tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar zuwa Kudu.

Akwai kungiyoyi daban-daban a Kudancin kasar nan da suke jiran babban taron jam’iyyar don yanke shawara ta karshe kan batun.

An yi imanin cewa idan Arewa ta samar da shugaban jam’iyyar, Kudu ce za ta fitar da dan takarar Shugaban Kasa a zaben 2023.

Akwai zargin cewa kafin zaben 2015 masu ruwa-datsaki na jam’iyyar sun cimma matsaya cewa za a mika tikitin takarar Shugaban Kasa ga Kudu bayan kammala mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Yayin da wadansu manyan ’yan siyasa kamar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Sani Yarima, suke cewa babu wannan yarjejeniya, masu son a mika takarar shugabancin kasa zuwa Kudu sun ce an kulla yarjejeniyar ce don tabbatar da adalci, a jam’iyyar tsakanin Arewa da Kudu.

Aminiya ta gano cewa don cimma burin mika mulki ga Kudu, babu dan siyasar yankin da yake neman shugabancin jam’iyyar, sun bar wa na Arewa su fafata a tsakaninsu.

Tarko ga burin Kudu na shugabanci

Wasu majiyoyi sun ce yawaitar masu neman shugabancin Jam’iyyar APC a tsakanin ’yan Arewa kan iya zama tarko ga mutanen Kudu.

Wata majiya ta ce, koda wani daga Arewa ya fito a matsayin shugaban jam’iyyar, ainihin yankin da zai samar da Shugaban Kasa zai bayyana ne kawai a karshen shekarar 2022.

“Ina fadin haka ne saboda akwai wadansu masu karfi a cikin jam’iyyar da ba sa son mulki ya koma Kudu.

“Don haka, akwai yiwuwar cire duk wanda ya fito a matsayin shugaban jam’iyyar daga Arewa, don fifita wani daga Kudu, kai koda a matsayin shugaban riko ne, domin tabbatar da ganin an samu dan takarar Shugaban Kasa daga Arewa.

“Wannan abu ne mai yiwuwa, domin yankin daya kan iya fito da dan takarar Shugaban Kasa da kuma shugaban jam’iyya.

“Don haka, mu jira mu ga wanda zai fito a matsayin shugaban kuma za ku ga inda abin zai kasance,” inji majiyar.

Masu neman shugabancin jam’iyyar daga Arewa maso Gabas

Sanata Ali Modu Sheriff

Gwamnan Jihar Borno na farko da ya yi wa’adi biyu a jere (2003-2011).

A shekarar 2003, ya yi takara a karkashin Jam’iyyar ANPP ya yi nasara. An sake zabarsa a 2007 a karo na biyu.

Ya kuma taba zama Sanatan Borno ta Tsakiya sau uku. Sheriff ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Jam’iyyar APC.

A zaben shekarar 2015, Sheriff ya koma Jam’iyyar PDP mai mulki.

Ya shaida wa manema labarai cewa matakin da ya dauka ya amfani kasar nan, ya kara da cewa a matsayinsa na Gwamna mai wa’adin mulki biyu da sanata mai wa’adi uku, muradinsa shi ne ya bayar da gudunmawarsa ga ci gaban kasa.

Daga baya wasu gwamnonin PDP da sauran masu fada-a-ji a cikin jam’iyyar sun gayyace shi don ya zama shugaban jam’iyyar na kasa bayan shan kaye da jam’iyyar tayi a zaben 2015.

Daga baya tsohon Gwamnan ya koma APC bayan rikicinsa da manyan jiga-jigan Jam’iyyar PDP, inda suke zarginsa da cewar dan leken asirin Jam’iyyar APC ne.

Abokan siyasarsa sun ce yana ji da kwarewarsa, a siyasa da karfin aljihu don ganin ya samu cim ma burinsa, ta yin amfani da matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar.

An ce Sheriff yana tuntubar masu ruwa-da-tsaki, yayin da kungiyoyi a cikin jam’iyyar ta APC suke ganawa da shi don fara yakin neman zabe.

Tsohon mashawarcin tsohon Gwamna Kashim Shettima kuma jigo a jam’iyyar, Mustapha Gambo, wanda yake cikin magoya bayan Sheriff, ya tabbatar wa Aminiya cewa tsohon Gwamnan zai bayyana niyyarsa ta neman kujerar shugabancin Jam’iyyar APC.

Shettima, ya taba zama Gwamnan Jihar Borno karo biyu, ya shahara a tsakanin mutane da yawa a shekarar 2011 zuwa 2019 lokacin da yake rike da madafun iko a jihar, wanda ake dauka a matsayin cibiyar rikicin Boko Haram.

Mutane da dama sun yaba masa lokacin da yake Gwamna, musamman gudunmawar da ya bayar wajen dakile ta’addanci da kula da ’yan gudun hijira.

Sai dai wadansu suna ganin yadda yake sukar gwamnatin Buhari na iya kawo masa cikas.

A watan Disamban 2020, an ji tsohon Gwamnan yana cewa, “Buhari ba Allah ba ne.

Idan akwai abubuwan da suke bukatar gyara, za mu yi masa nuni da su daidai gwargwado kuma ba tare da wata shakka ba.

Duk da tayar da kayar baya, ya yi nasarar magance wasu matsalolin ci gaban jihar.

A watan Fabrairun 2019, aka zabe shi a matsayin Sanatan Borno ta Tsakiya, inda ya maye gurbin Sanata Baba Kaka Bashir.

Duk da halinsa na yin magana da shugabanni tun daga zamanin da yake Gwamna, ga dukkan alamu Shugaba Buhari yana ba shi girma.

Musamman idan aka yi la’akari da jinjina da yake masa, wanda ko a kwanan nan da tsohon Gwamnan ya yi bikin ranar haihuwarsa sai da Shugaba Buhari ya ce: “Ina alfahari da Shettima saboda nasarorin da ya samu a ofis a matsayin daya daga cikin gwamnonin da suka yi fice a Jam’iyyar APC.

“Duk da kalubalen tsaro, ya samu damar yi wa al’ummarsa aiki da kuma cika manyan alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

“Za a tuna da Sanata Shettima saboda abubuwa da yawa, ciki har da yadda ya mika jihar ga Farfesa Babagana Zulum, wanda zai iya maye gurbinsa.”

Danjuma Goje

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe ne kuma Sanatan Gombe ta Tsakiya tun daga 2011.

Tsohon Gwamnan, wanda ya janye daga takarar Shugaban Majalisar Dattawa don bar wa Sanata Ahmad Lawan kwanaki kadan kafin kaddamar da majalisa ta tara bayan shiga tsakani da Shugaba Buhari ya yi, yana daya daga cikin wadanda ake jin suna hararar kujerar shugaban jam’iyyar.

A matsayinsa na jigo a kafa jam’iyyar, Sanata Goje yana samun goyon bayan abokan aikinsa a majalisa da wajenta.

A wata hira da aka yi kwanan nan, Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige, ya ambaci Sanatan a matsayin daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar.

Masu sharhi sun ce watakila tsamin dangantakar da yake tsakanin Sanata Goje da Gwamna Inuwa Yahaya na iya yi masa tarnaki wajen lashe kujerar shugaban jam’iyyar.

Sanata Goje da Yahaya suna jayayya a kan iko da jam’iyyar a jihar gabanin zaben 2023.

George Akume

Sanata Akume, wanda ya yi wa’adi biyu na Gwamnan Jihar Benuwai, shi ne Ministan Ayyuka na Musamman da kuma harkokin gwamnatoci a yanzu.

An ce yana daya daga cikin masu fada-a-ji da kuma damar samun shugabancin jam’iyyar ganin kusancin da yake da shi da Shugaba Buhari.

Ya wakilci Benuwai ta Arewa maso Yamma da aka fi sani da Zone B, a Majalisar Dattawa. Shi ne Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar daga Yuni 2011 zuwa Yuni 2015.

Wata majiya mai tushe da ke kusa da Akume ta shaida wa Aminiya ta waya cewa wadansu manyan ’yan siyasa a Jam’iyyar APC sun bukaci Ministan ya shiga takarar shugabancin jam’iyyar.

“Sanata Akume zai tabbatar da jam’iyyar ta hanyar motsa ta saboda ya jajirce a kan manufofinta kuma ya yi aiki tare da Shugaban Kasa.

Idan masu ruwa-da-tsaki na Jam’iyyar APC suna ganin ya kamata ya jagoranci wannan tafiya to zai kasance ya yi hakan.

Kuma a shirye yake ya karbi duk wani aiki da jam’iyyar za ta ba shi,” inji shi.

Amma har yanzu Akume bai yanke hukuncin zai tsaya takarar ba. Sanata Tanko Al-Makura Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, mamba a tsohuwar Jam’iyyar CPC da ta narke a Jam’iyyar APC.

A Watanni da suka gabata, Gwamna Abdullahi Sule, ya bukaci sauran kungiyoyin da su tallafawa jihar don ganin ta samar da shugaban jam’iyyar na gaba.

Amma an yi imanin cewa gayyatar da Hukumar EFCC ta yi wa Sanatan a watan Yuli na iya shafar damarsa ta samun tikitin takarar shugabancin jam’iyyar.

Sai dai tsohon Gwamnan ya musanta zargin almundahana a kansa.